Kishore Kumar Hits

Hausa Soundtrack - Zana Rayu текст песни

Исполнитель: Hausa Soundtrack

альбом: Zana Rayu


Sona ne fah
On the beat

Da ke za nayi rayuwa
Kece mallaki na, kin zam mini garkuwa
A dare da rana
Da kai za nayi rayuwa
Kaine mallaki na, ka zamto min garkuwa
A dare da rana

Taho sahiba ki zo ta waje na
Kina nan a rai dare har rana
Cikin zuci so yake min kuna
Shiya saka nace bazan zauna ba
Zo zana furta
Burina ki fahimta
Kice dani masoyin ki
Abba gun ya'yan ki
Madubi gun ki
Mai sona bazan ki in amsa ba

Maza-maza zo nayi ma tarba, tunda kaine zabi na
Da kai zamu yo taba-taba, masoyi zo ga gu zauna
Da kai zana ba so har kauna, tunda ka cika burina
Kaine kayi dashe a cikin raina
Kai zan ba wa dukkan sirri na
Sirri na so kuce mini kauna ce
Rabo da kai bazai yimin kyau ba

Zancen ki hakkun, sam ba wani shakku, son ki a rai ya kekkewaya
In zanyo bayani, kece nayi yakini in kika barni zan sha wuya
Jani, kai ni
Birni na masoya, gaki garen bazan fadi ba

Gani ga masoyi na
Mai share kuka na
Rufin asiri na
Uba ga ya'ya na
Zuciya tana kuna
A rashin habibi na
Kai zanyi wa kauna
Dare ko da rana
Mun zama jini da hanta
Mai raba mu zai wahalta
Mun sha lahaula mun wuce masu gaba

Da ke za nayi rayuwa
Kece mallaki na, kin zam mini garkuwa
A dare da rana
Da kai za nayi rayuwa
Kaine mallaki na, ka zamto min garkuwa
A dare da rana

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель