'Yan mata mai ya faru? Mai ya faru? Yau dai ba kiyi mini zance ba Wanene ya taban ki? Ki nunan shi idan bai ga fushi na ba Ba kaine ba masoyi Kaine yau baka kawon chocholate na ba Kanwata kiyi hakuri Rigimar ki kamar ba'a gama raino ba Ni sai ka goya ni, a kafadar ka Ko kuma kayi mini bambu, ko kuma inki shiru Dukka abinda kike so, haka zanyi Kauna bata zama laifi ba Nayi dace da masoyi, dan yayi Guna bai gaza raino ba Nine daya na biya ki, kuma na iya ki Rikon ki bazai zama kowa ba, yanmata na Musha kauna yarinya, musha kauna Musha kauna duniya labari ce Musha kauna dan yaro, musha kauna Musha kauna duniya labari ce ♪ Na zama sirikar umma, sirikar baba Su suka haifa min miji mai gyara zaman duniya Na zama sirikin baba, sirikin mama Su suka haifo min baby mai saita zaman lafiya ♪ Duk inda kaje Rabbana ya kare ka Ka dawo mini lafiya ka zo mu kasance Bana so mata su kalli fuskar ka Duk wacca ta kalle ka Allah sa ta makance Ko sun kallen ma ba zana gane ba Duk inda naje son ki ne yake bina Kuma duk inda naje ji nake kina ji na Ko wata na gani ke kike gizo a bisa idaniya ♪ So mai son ka, ka more soyayyah So mai son ki, ki gane soyayyah Son mai son wani yana ban tsoro ne Ni dai na sani son maso wani cuta ne Ni dai na sani masoyi dadi ne Nima na sani masoyi dadi ne Ni dai ga tawa nan da nake riritawa Ke nake fifitawa Kinfi kowa tawa Yar dimurmur tawa Yar dimurmur tawa Dimurmur Yar dimurma tawa