Kishore Kumar Hits

Sadiq Saleh - Darasul Auwal текст песни

Исполнитель: Sadiq Saleh

альбом: Darasul Auwal


Bakin ciki garen ya kare
Farin ciki garen zai dore
Samun ka tabbacin na more
Mata cikin ku ni na kere
Ina son ka
Allah ya mallaka min kai har abada
Kai ne
A Darasul Auwal darisi na farko
A soyayyah sai dai darasu thani, mun gama babin nan
A Darasul Auwal darasi na farko
A soyayyah sai dai darasu thani, mun gama babin nan
Hubbi, hubbi
Hubbi, hubbi na
Kalbi, kalbi
Ruhi, ruhi
Ana

Zana raka ki a duk nisan tafiya, sai mun dawo
Inta tsare ki kaman sirrinta gyada, murfi bawo
Ga nasara ta mika hannayen ta, sai mun jawo
Munyi shirin mu shige babban lamari, kafa mun sawo
Ilahu nagode maka, da kabani yar baiwa
Sirri na rai ya habbaka, har yakai ni furtawa
Da son ki ma ni zan mutu, bazan iya in rabu dake ba

Cigaban ka nake so baby na
Daga hannu hubbi na
Addu'a zanyi maka zabi na
Komai nace maka ce "ameen"
Ya Ilahi ka taimaki wannan bawan (ameen)
Ka tsare shi da duk sharrin mai sharri (ameen)
Ka hada shi da mara adadin alkhairi (ameen)
Ka cika mishi kyakkyawan kudirin shi (ameen)
Rufa mai asiri, yafi karfin bashi (ameen)
Ka kaishi gaba, makiya ka kai bayan shi (ameen)
Kasa in zamo mallaki, matar shi (ameen)
Karshen zance Ilahu ka amsa, Allah ameen

Ni kin gama min komai
Kina son kallo na
In hadu dake yafi
Kina kure dadi na
Madubin kallo na
Da son ki nake kwana
Zo cika burina karda mukai ruwa rana
Hakar da muke dake, kyanta ta cimma haka yafi
Ina tsoron mutuwa in tafi in bar ka wayyo
In daina ganin kyakkyawar fuskarka oh-ohh
Tsoka jini, gangar jiki a ruhi daya
Kaine kadai, mai mallakin ta zuciya
Mun zama daya, soyayyah ni da kai ba rabuwa

A Darasul Auwal darisi na farko
A soyayyah sai dai darasu thani, mun gama babin nan (tabbas)
A Darasul Auwal darisi na farko
A soyayyah sai dai darasu thani, mun gama babin nan
Mun gama babin nan

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель