Jaruma, jaruma ♪ Jaruma kina lokaci bana banga tamkar ki ba A zahiri akwai tabbaci ba za'a taddo ki ba Jaruma ina lokaci, jaruma nike lokaci ba za'a chanza ni ba ♪ Eh, soyayyah take sanya yaro ya makance Watarana yazo a baro a kurumce Duniya ta baka jindadi a takaice Wataran ta saka jin haushi har ka mance Nayi nawa sai naka yaro Lokaci yazo babu kwauro Rayuwa takan zo da sauyi ko wani yanayi Maza ka rungume kaddara zaka guje wa laulayi Jaruma ni ce Kece a kan kaddamin ki Jaruma suna anka baki Duk masu ja zasu barki Su ko masoya su biki Kece nawa tambari Don ki fito ki ja ayari Soyayyah zan baki rike min Sirri ne daga zuci aje min Jaruma ina lokaci Jaruma nike lokaci ba za'a chanza ni ba ♪ Jaruma na baka zuciya ta rike Adana ta a nesa bani so kayi sake Mallaki a gare ka ga tukuici rike Duk mafarki nayi baka take zan wartsake Damuwa na daina yi Duniya da ni takeyi Zuci kai tayi ra'ayi da soyayyah Ta adana ka a gefe baka jin kunya ♪ Ke na rike kadai gwana ta da zuciya daya Domin ki ne ko babu niyya ni zanyi dariya Kina da kyau kin kera mata aji da kwalliya Wasu su kan kira da sunan ki salo na zaulaya Taho ina kike? Fito su gano ki, ba gani nan ba Yi masu tsere ya da tutar yaki, ba gani nan ba Gani gaban ka Na amsa sunan ka Soyayyah ni ban da tamkar ka