Kishore Kumar Hits

Abdul D One - Asha Zuma Maman Dady текст песни

Исполнитель: Abdul D One

альбом: Asha Zuma Maman Dady


Asha zuma a sha sikari kowanne yana da dadin sa
Gari-gari akwai mata, kowacce tana da sunan ta
Kuma dukan su mata ne kowacce tana da halin ta
A cikin su akwai wacce tayi daban babu mai irin nata
Mai hali gidan kyauta, da ka ganta tsaf akwai tsafta
Ko'ina idan ta je, da ta wuce ayi ta neman ta
Matar mutum daya ce tal na saba wake sunan ta
Daga ke ba kari hajajju, kai kun ji taken ta
Yar Aljannah sunan ta
A gurin mijin nata
Lallai ta ci sunan ta
Don na yaba da kyautar ta
Shiyasa na ce barka da sallah gare ta zan furta
Da ita da ya'yan ta
Kai harda ma mijin nata
Wace ce wannan, wace ce? Toh zan kirawo ta yanzu
(Ayyeah kai)
(Ayyeah kai)
(Ayyeah kai, ah-ah, ah-ah)
(Ayyeah kai)
Maman dady barka da sallah
Maman dady daga ke ba kari
Maman dady barka da sallah
Maman dady daga ke ba kari

Assalamu alaikum hajajju, na zo gaishe ki
Gaisuwa ce ta musamman da ke da iyalan ki
Ma'ana ya'yan ki, kai harda mijin na ki
Ikon Allah sai kallo, mun basu mamaki
Hajiya giwar mata, maman dady a gaishe ki
Kin amsa sunan ki
Sarauniyar mata Allah sarki ya ja da kwanan ki
Kin girma yanmata a cikin su wa zata kamo ki?
Ruwa ga ki ga daki
Sannan ga diyan banki
Mama a gaishe ki
Waka banyin irin ta ki
Matar Suleiman Danwawu ana kwatancen ki
Maman dady da anisa sam ba a kamo ki
Maman yaya Muhammad kyauta ba irin ta ki
Matar Suleiman Danwawu mai sa maza aiki oga
Maman dady barka da sallah
Maman dady daga ke ba kari
Gida-gida na je ammah sam ba irin naku
Kyatuttuka an min kyautar sam ba irin ta ku
Kudi-kudi an ban ammah sam ba irin naku
Kuna da kyan hali bako ya zam abokin ku
Kuna kulawa da mutane da ku da ya'yan ku
Sannan kuna son al'ummah komai kuna basu wayyo
Maman dady barka da sallah
Maman dady daga ke ba kari
Maman dady baiwar Allah (ga mama)
Maman dady mai son Allah (ga mama)
Maman dady mai tsoron Allah (ga mama)
Mai kyauta don Manzon Allah (ga mama)
Matar Suleiman Danwawu (ga mama)
Matar Suleiman Danwawu daga ke ba kari
Danwawu
Danwawu
Danwawu
Suleiman Danwawu
Maman dady barka da sallah
Maman dady daga ke ba kari
Maman dady barka da sallah
Maman dady daga ke ba kari

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель