Kishore Kumar Hits

Auta Waziri - AMARYA текст песни

Исполнитель: Auta Waziri

альбом: AMARYA


Yauwa
Auta Waziri kuke ji malan
Its d daski ovizta on the beat
Amarya kin ci gari kin bar gishiri kin zama sukari
Kin dauke ado na fada kin sa mata sun zaga gari
Kece akace yar nan data sanya iyaye alfahari
Nasarar ki tasa mata suka rude kin samo nagari
Angon ki abun fahari kin samo wanda kike kudiri
Zabin ki amarya shine zabi na iyaye kiji
Ladabi da biyayya ki yi wa ango sam karki gaji
Daza kuji mata kan amaryanan mi anka fada
Dawisu gwana ta ado nasarar maiko ma na a gyada
Kwarya tabido kwarya tabido akushi sai tai zarya
Mai noma acikin ruwa je kufada masa baya bidar kunya
Mai kishi da amarya kar ta matso kusa bar ta acan baya
Kinci tuwo da miyanki amarya kin bar wasu na cin gaya
Lokaci naki (mmmmm)
Amarya ga mijinki nan ango shi akaima gara
Anshaida an bashi ke zaki gidansa me ya saura
Daure karki tsallake umarni na sa ki gyara
Aljanar ki na kasan tafi na mijinki sai ki lura
Komai kinka ayyana
Kafin ma ki bayyana
Shaidawa mijin ki in yace a'a kibar shiga shawarina
Mata adon gari (ayya kai)
Kune adon gari mata
In baku ba gari in kun yawa kusa zullumi mata
Ni zan ware lokaci kan inji miye bukatuwan yan mata
Ana batu na aure ne in kin yi shi kin cike yar gata
Idan da saurayi ki rike shi nace kar ki bai wani rata
Aure kawai kuyi shine darajar ki autar mata
Mata adon gari
Kune adon gari mata
In baku ba gari
In ku yi yawa kusa Zullumi mata
Mata mata ga amarya ga angonta
Mun lissafa ango shine jigonta
Dama dama wataran dama dama
Kuji ance sun samu diya dan tatata
Ki tsabta kinji amara ki girki madallah
Ba shi ruwa angonki nasan bai sa ki kwalla
Toh daure kinga diyar girma yau sai madallah
Kin dace da ango dan girma toh Alhamdulillah
Kai tufawa amaryanan mai kyau da ado dawisun ce
In ta fito sai muji nata sun dauka kowa zance
Suna ta fadi sunga amarya ga sarkar zinari ce
Wasuma sun rude kayanta atampa ko kuma leshi ce
Toh da na waiga ni mai waka nagano alkyabba ce
Mai hoto dan Allah daukarni in dan kafa hujja ce
Tunda naganku guri na bikinan nasan sai an tantance
Damsu da kokas kuka kware a fannin yin hoto
In dai hoto ne na amarya har angon sai an kalla
Dama dai dan Allah zanzo ni ku koya min hoto
Amma dai ga amarya ga ango nan na zaune
Naga kwayaye naga iyaye yu duka na tattakawa
Naga abokokai na gurin ango dada yu na juyawa
Naga kudi naga ruwan naira da dala an sanyawa
Munga ado munga zubin mata duka dai kyawawa
Matan arewa ne mun san
Matan kasar mu ba dama
Mun san kudin kasar nan ma
Girman su wallah ba dama
Amma akwai kananu ma wanda zasu baku dan dama
Allah yasanya aurenan yayi Albarka ango da amarya
Auta waziri kuke ji malan

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

YBN

2022 · сингл

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель