Kishore Kumar Hits

Auta Waziri - Soyayya текст песни

Исполнитель: Auta Waziri

альбом: Soyayya


Ashe so da dadi yake
Soyayya
Ashe so da daci yake
Soyayya
Idan har ka dace da wanda yake san ka
Rike shi da gaskiya yake

Ashe so halitta ne cikin zukata
Da kadan 'dada girma yake
Soyayya
Misali na hanta da jini suke zaman tare
Rabuwar su wuya dai take
Soyayya
Cutar so idan har ya kama wasu zukata
Baitun magani sassake
Soyayya
Amma so da dadi yake
In ka dace da wanda yake san ka da gaske ba da wasa ba

Ku shaida wa mai so
Ya shiga duniyar so
Ya gane yadda shi so yake
Soyayya
Idan yau da dadi
Gobe babu dadi
Batun nan ku ce haka yake
Soyayya
Ku saba da juna
Kamar babu ranar
Da za ai rabo ko a dake
Soyayya
Abun al'ajab sai cikin so idan kayi
Ka ban bance kwarya da zuma
Ga misalai

Da ciwo ka so wanda baya nuna soyayya
Idan ya ganka sannan ya tina
Soyayya
Idan ka bashi rata
Mu'amala da mata
Shi bai gudun abun ai magana
Soyayya
Ku gane duk batu na
Dare nace da rana
Mazan garin mu
Ku ne na tina
Soyayya
Duniya makaranta
In ta nai ma wasu gata
Wasu sai ta daura su kaya ga dalilai

Naga yarda so ya maida mai tunani
Naji yadda zai rude a yan sakanni
Naji yadda so
Yake bugun zukata
Naga yadda so yake silla na kyauta
Naji yadda so yake sillar a rayu
Naga yadda so yake kisan marayu
Shi dafi na so
Kunga ba a mai iyaka
Wani lokacin ma ya sa a karya doka
Kunga yadda so
Yake sillar zaman ta
Kunga yadda so yake rikon makota
Kunji hudubar so
Akwai gashi da dama
In nace na zano su
Zamu kwana zaune

Soyayya, so
Kaso mai san ka
Soyayya, so
Eh, kaso mai san ka
Soyayya, so
Nace kaso mai san ka
Soyayya, so
Kaso mai san ka

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

YBN

2022 · сингл

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель