Kishore Kumar Hits

Auta Waziri - Sarkin Bichi текст песни

Исполнитель: Auta Waziri

альбом: Na Taka Kaya (Album)


Uhm, yauwah
Auta Waziri kuke ji malam
Mai martaba
Wa zai taba?
Sarakin garin mu wa yayi shi ado?
Ruwan sama
Kuma kurtun zuma
Daga kai angama, saraki mai al'umma
Sarkin Bichi, kuma mai son Bichi
Jinin Bayero kaci ayi ma hidima
Ga dan Bayero
Nasiru Ado Bayero
Zauna mai martaba, tamkar Ado Bayero
Ba sai an nesanta kalamai ba (kai!)
Zauna Sarkin Bichi, tamkar Ado Bayero
Ba sai an nesanta kalamai ba
Zauna Sarkin mai martaba, tamkar Ado Bayero
Ba sai an nesanta kalamai ba
Dafa Allahu buwayi sarkin iko
Gyara Allah makadaici mai fifiko
Dafa aikin muka dosa
Muna so ne tayi rassa
Dafa dan darajan dan Amina
Za muyi wake zancen duniya
Wakar sarki Nasiru Ado Bayero ne
Nasan in kunsan haka shi Sarkin Bichi ne
Sannan dan sarki marigayi Ado Bayero ne
Dan sarki shike sarki
Ga Sarkin Bichi nan gwanki
Mai karfi daukan nauyi
Ga gwanki makashin gwanki
Dan sarki shike sarki
Ga Sarkin Bichi nan gwanki
Mai girma dan mai girma
Mai gona shike noma
Dan sarki shike sarki
Ga sarkin Bichi nan gwanki
Mai nasaba dan alfarma
Masu muhibba dan girma
Dan sarki shike sarki
Ga sarkin Bichi nan gwanki
Yau makiyan ka suna baya
Barsu saraki su sha haushi
Dan sarki shike sarki
Ga sarkin Bichi nan gwanki
Duk girman Giwa a dawa
Zaki aka bai sarki
Dan sarki shike sarki
Ga sarkin Bichi nan gwanki
Nasiru Ado Bayero ne
Mai masu na gaban sarki
Dan sarki shike sarki
Ga sarkin Bichi nan gwanki
Ga talakan shi a dama nai
Baya hana su, su zo nema
Dan sarki shike sarki
Ga sarkin Bichi nan gwanki
Shike basu makwanci
Ga gona nan suyi noma
Dan sarki shike sarki
Ga sarkin Bichi nan gwanki
Basu kudi
Kuma basu abinci ko suturan da suke nema
Dan sarki shike sarki
Ga sarkin Bichi nan gwanki
Nasiru Ado Bayero
Sarkin Bichi na Kanon Dabo
Matan Kano, kusha madara ga zuma
Dadin Kano akwai Sarkin al'umma
Ga mai mulkin mu Nasiru dan Bayero
Matan Kano ku taso kuyo rawa da dadi
In tamburan ga sun kai zan zo wajen da fadi
Matan Kano, kusha madara ga zuma
Dadin Kano akwai Sarkin al'umma
Ga mai mulkin mu Nasiru dan Bayero
Na zo Kano a tun wuri don zana gaida sarki
Mai ajiyar Allah ka fisu karfi
Dadin zuma a sha kuma har
Hadarin cida, ka taso kai daya ka kauda rana
Tsawa kake, ashe ka ratsa zuciya na kurma
Sarkin Bichi, ka fisu ado kuma ka fisu kudi
Jinin Bayero, a basu dollar kuma a basu jirgi
Ya kai su garin can da zasu kwana
Mai martaba, Allah tsare kuma ya kara girma
Sarkin Bichi, mai tagwayen masu Allah ja da kwana
Gasu auta sun zo tambari suyi ma
Matan Kano, kusha madara ga zuma
Dadin Kano akwai Sarkin al'umma
Ga mai mulkin mu Nasiru dan Bayero
Kai sai na tuna da sarki dan Bayero
Allah jikan uba
Wanda bai da fargaba
Shike sahun gaba
Don ci da al'umma
Ado Bayero
Kowa nata kuka, ana Allah jikan Ado Bayero
Sarki, Sarkin Kano
Bayan baba kenan, ba'ayi kamar sa ba
Sai Sarkin Bichi nan Nasiru Bayero
Zauna Sarkin Bichi baban kowa (baban kowa)
Sannan ka cika da rumbun baiwa (rumbun baiwa)
Kaine mai al'umma, sannan kai hidima
Sarki bashi da tsoron kowa
Kuma sarki bazai so yaji zancen karya ba
Kuma sarki bazai kyamaci al'umma tai ba
Kuji sarki baya boye marayun duba
Nasirun dai Ado Bayero kyakkyawan Sarki
Zauna Sarkin Bichi baban kowa (baban kowa)
Sannan ka cika da rumbun baiwa (rumbun baiwa)
Kaine mai al'umma, sannan mai hidima
Sarki bashi kuma bashi da tsoron kowa
Kuma gashi da rumbun baiwa
Kuma gashi fari ma dogo
Waka daya baban sarki
Sauran ka bari sai nazo

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

YBN

2022 · сингл

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель