Kishore Kumar Hits

Auta Waziri - Ga Labarina текст песни

Исполнитель: Auta Waziri

альбом: Ga Labarina


Labarina, ga labarina
(Prince production)
Ga labarina sai ki saurara
In har kin yarda in zama angonki
Ga labarina sai ka saurara
In har ka yarda na shiga dakinka
Zo ki dan zauna don mu tautauna
Ko cikin raina baniyin barna

Har cikin raina
Kai na ba kauna
Kai ka zaga ta duka sashe na
In akai zance raba mu kwai barna
Gara ma abar mu ni dakai mu sasanta
Ga labarina sai ki saurara
In har kin yarda in zama angonki

Ni a ko yaushe ina bukatar ki
Dukanin zance muyi a dakinki
Alkawar kenan tsare mutuncinki
Tunda kin yarda na zama angonki
Ga labarina sai ka saurara
In har ka yarda na shiga dakinka

Gaskiyar zance
Kai na tantance
Kaga so dani dakai gare ni hujjace
Inka lamunce
Sai na alkince
Ni kadai dakai abar mu ba'a ma kwace
Ga labarina sai ki saurara
In har kin yarda in zama angonki
Ga labarina sai ka saurara
In har ka yarda na shiga dakinka
Kin ka ban sako
Sai nazam bako
Shi ruwan randa sai da dan koko
Kinji yar auta ke nake roko
Karki bada ni so ya kada ni
Ga labarina sai ka saurara
In har ka yarda na shiga dakinka

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

YBN

2022 · сингл

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель