Kishore Kumar Hits

Auta Waziri - Alqar So текст песни

Исполнитель: Auta Waziri

альбом: Alqar So


Auta Waziri kukeji malam
(Mahmoud MG on the beat)
Da dadi soyayyah
Kuma da daci soyayyah
Alaqar da ake a ciki wataran kan sa ayi jinya
Da dadi soyayyah
Kuma da daci soyayyah
Alaqar da ake a ciki wataran kan sa ayi jinya

Watarana in za'a fada mini nikam zan ce "a'ah"
A zato na nayi damaran soyayyah kuma na shirya
A gaba na sai a tisa, wani sa'in ma harda rada
Kuma bana gane nufin sa bare ma na chan kurya
Haka ya sa ko magana aka min sai in kama fada
Kwakwalwa ta rikida fushi na ya cimma wuya
Abin tamkar zana bari kamar sai na sake shiri
Ashe mata ke da zani maza su ankayi wa nadi
Da dadi soyayyah
Kuma da daci soyayyah
Alaqar da ake a ciki wataran kan sa ayi jinya
Sai na gano dadin magana in akayi tauna tun a baka
Kafin ma ayi furucin sa yazo kunni har ka jiya
Bari mai sauraro ka tsaya bana nai nisan ajiya
A cikin so nai jimirin, gaya falke bana gajiya
Na samo 'yar da ta ke nunan so kullum ta dada
Idan har mun hada ido ta ita komai sai ya tsaya
Kamar shuka ne a kaya iri zaiyi wa sakiya
Ruwan teku ba'a haka shi da gulbi kun san da haka
Da dadi soyayyah
Kuma da daci soyayyah
Alaqar da ake a ciki wataran kan sa ayi jinya

Da dadi soyayyah
Kuma da daci soyayyah
Alaqar da ake a ciki wataran kan sa ayi jinya
Ashe so kan sa cigiya, yayi ma daurin igiya
Ka zamto tamkar zakaran da cara ke mai wahala
Gaya ashe akeyi wa miya, akan so tunu nayi aniya
Idan har ke zana raka toh komai ma zana kula
Kamar zahra inga wata da haske sam babu bata
Shigar girma kinka iya gwana ta kin bada kala
Idan har kin ce, "Na bari" ashe kin sa min matsala
Dake komai nawa yake tafiya bana so mu tsaya
Da dadi soyayyah
Kuma da daci soyayyah
Alaqar da ake a ciki wataran kan sa ayi jinya
Haka nasan za a rina watarana zaka tuna
Soyayya sai jajurtacce shine zaya iya
Idan har kayi nasarar so sam-sam ma karka sake
Da zafi komai wahalar sa kace, "Wai kai kayi gajiya"
Jarumtan naso ka gwada a filin yaki ka tsaya
Idan har ka so ni da gaske in gano ka shirya
Da farko kayi min magana munshari in zaka tuna
Ammah yau na amsa kiran ka ka juyo gwarzon zakara
Da dadi soyayyah
Kuma da daci soyayyah
Alaqar da ake a ciki wataran kan sa ayi jinya
Da dadi soyayyah
Kuma da daci soyayyah
Alaqar da ake a ciki wataran kan sa ayi jinya

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

YBN

2022 · сингл

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель