Kishore Kumar Hits

Auta Waziri - Farin Cikina текст песни

Исполнитель: Auta Waziri

альбом: Farin Cikina


Auta Waziri kuke ji malam
Beats Ali's production
Farin cikinki shine farin cikina
Ki bar gudu na ba inda zana zauna
Farin cikinka shine farin cikina
Kabar gudu na ba inda zana zauna
Kina taba ni
Kina yawwan tsuma ni
Ina kike ne kawai kirani zani
Abar fadi na kice kawai a raina
Kin sanya kauna tana yawwan zigani
Ki bani dama kawai ki bani soyayya
Mu sanya yarda kar ayi mana rauni
A kanki ne ma suke ta nuna ki
Soka baya gabana ina ta nuna soyayya
Farin cikinka shine farin cikina
Kabar gudu na ba inda zana zauna
Farin cikinki shine farin cikina
Ki bar gudu na ba inda zana zauna
Idan da hali karka barni dan arziki
Kazo mu zauna kai kadai naba lokaci
Ina da dama dazana so su ma sai naki
Suna ta bina naki yanzu sai tsokaci
Kawai ka gano ko wata rana kaje biki
Saboda mata ko dan abinci ma karka ci
Ina da kishi akanka shiyasa zanaki
Awa guda cur idaniya basa ganka ba
Bazan iya ba
Farin cikinki shine farin cikina
Ki bar gudu na ba inda zana zauna

Sanki yakai munzalin da ban son fada
Ko na fada ma baza'a gane karshen sa ba
Ki gane cewa a sanki ni ko ban farga ba
Ba zan iya ba da wata in bazan ganki ba
Jinin jikina da naki sun hade gu guda
Wa zai raba su cikin kasar ga ban ganshi ba
A kanki zani duniyar da ba namu ba
Indai kina nan nasani bazan bata ba
Farin cikinka shine farin cikina
Kabar gudu na ba inda zana zauna
Farin cikinki shine farin cikina
Ki bar gudu na ba inda zana zauna
Kaine a dama na baza ka kauce ba
Waninka ko yazo bazamu saba ba
Kasan da soyayya sai anyi hakuri ma
Zama na rayuwa ma ya baza'a saba ba
Zan samu nutsuwa ma in kana zama gurin na
Farin ciki yakan zo ya bazana gode ba
Kawai ka yarda rabbi ya hada ni dakai
A lamura na zanso ace kazamto gaba
Farin cikinki shine farin cikina
Ki bar gudu na ba inda zana zauna
Farin cikinka shine farin cikina
Kabar gudu na ba inda zana zauna

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

YBN

2022 · сингл

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель