Kishore Kumar Hits

Auta Waziri - Hajiya Ta текст песни

Исполнитель: Auta Waziri

альбом: KEWA ALBUM


Auta Waziri kuke ji malam
Ahya
Ina ji dake
Kina ji dani
Idan babu ke
Kamar babu ni
Ciwon sanki ne
Zo ki ban magani
In sha inji sauki ki samar dani
Akwai lokaci a dukan zamani
Da soyayya na taho kimin lamuni
Cikin masu sanki yau ki sanya dani
Kiban hankalinki karki basar dani
Akwai kyau gareki kinyi mun kwar jini
Mafarkinki na dade dayi tintini
A sanki yakai ga bani ji ban gani
Kin zamo jijiyar jiki na hanyar jini
Dake zanyi rayuwa
Ba da damuwa ba
Uhm hajiya ta (hajiya ta)
Kece hajiya ta (kece)
Hajiya ta
Kece hajiya ta
Ah hajiya ta
Kece hajiya ta
Hajiya ta
Kece hajiya ta
Haba masoyiya, bazan barki ba
Na dan bincika banga tamkarki ba
Wazai ganki inda ransa bai soki ba
Idan gaki zahirinki ba gaibu ba
A samun kamarki kila sai nan gaba
Idan za a dau dubu basa kai ki ba
Kwar jini da hankali basa fiki ba
Babu mai aurenki yayi miki kishiya
Nasarar samunki ya wuce dukiya
Kin wuce masu kinki ko a kyan zuciya
Mai farin ido ga ado zinariya
Ni a kaunarki na mace bazan sauya yanayi ba
Hajiya ta
Kece hajiya ta (eh)
Hajiya ta
Kece hajiya ta
Hajiya ta
Kece hajiya ta
Hajiya ta
Kece hajiya ta
Toh ina zaki je bakya fada min naje dake ba
Naga fura da nono banga ludayi ba
Naji so a rai ake saka shi bada wai ba
Ya zaki kula dani ban kula dake ba
Zinariya a mata basu kai ya ke ba
Ni ke nake gani
Koda a sansani
Guri idan dani
Bakya bidar wani
A sanki dai nake gini na kare rayuwata
Uhm hajiya ta (hajiya ta)
Kece hajiya ta
Hajiya ta
Kece hajiya ta (Ahya malam)
Hajiya ta (Ahya malam)
Kece hajiya ta (ahya malam)
Hajiya ta
Kece hajiya ta
Hajiya ta
Kece hajiya ta
Hajiya ta
Kece hajiya ta

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

YBN

2022 · сингл

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель