Kishore Kumar Hits

Auta mg boy - Tunda Ina Sonki текст песни

Исполнитель: Auta mg boy

альбом: Tunda Ina Sonki


AMG boy record
Tunda ina sanki zuciyata ta kamu
Bani barinki ko zanyi kwanan tsakiyar ruwa
Nifah fah ina sanka zuciyata ka saka
Daga zuwanka har gashi ka dauke kowa
Eh mana

Da dadi ka nuna so koh da idanu
Kwatancen gidanku kimin sanu a sanu
Da nazo ruwa kiban hanu da hanu
Kalamai na so nazo zana bajewa
Jin dadin masoyi shine a kula shi
Sanan yai abin yabo kuma a yaba shi
Kalamanka su suke kore haushi
A kaunarka zuciyata ta kafewa

Gidana ki san kece farko
Ki kwanta a zuciyata kiyi karko
Sadakinki koh miliyan nawa zan aiko
Na turo gidanku dan ai mana baiko
Allah dai ya sanya alkhairi
In same ki ne cikar buri
Ina sanki ba gudu ba ja da baya
A raina zama dake ni na shiryo

Uhm na shiryo

Tunanin ka shi yake deban kewa
Cikin zuciyata kai daya ba kowa
Amince dani da kai mun kulla
Ba ranar rabo dakai kaji dan baiwa
Kulawa gareka zan nuna
A ranar bikin mu ai dinner
Fushi in kayo dani ban jin dadi
Mun shiga so a ka'ida ba kutsewa

Rufe ni ki saya ni ki saya ni ki boye ni
Kana da mutuncinka kalaminka ya burge ni
Da kinyi shiga taki na kalla sai ta ruda ni
Ni banda irinka hanyar so kai ka daura ni
Idan tafiya tai tafiya toh karki share ni
Kaima kasani yarda ce karka yimin rauni
Na yarda dake kinga kina yi mini amfani
Da dadi kalmominka suna dada dadana ni
Ruwa yayi ruwa sanyi ina zaki saka ni?
Ni nazama bargo ka sha dumi kaine sarki

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель