Kishore Kumar Hits

Auta mg boy - Kije Dani текст песни

Исполнитель: Auta mg boy

альбом: SAIMA RANAR (Ep)


(AMG Boy Records)
Kije dani duk inda zaki je
Dani dake ba wanda zai raba mu
Kaje dani duk inda zaka je
Mun shaku ne ba wanda zai raba mu
(Eh mana)
Ba wanda zai raba
Rabbana, Rabbana, Rabbi shi ya hada
Wanda yace a raba toh dashi zan fada
Zaki zo ne? Don son ki naji yayi min rada
Zanyi waka ke dai kawai ki sanyo kida
Duk kalaman da zanyi ke kike shimfida
Don cikin masu son ki ba yani kin sani

Naga zahirin kauna kiri-kiri
Ba kamar yakai abin alfahari
Tunda ni da kai mun doki tambari
Wataran biki za'ayi ayiri-yiri
Shiko mahassadi mu kyale ja'iri
Zan fa bin gaba don nawa jarumi ka kai (jarumi ka kai)

Gaskiya, gaskiya so ya kama ni
In na kauce a hanya ka saita ni
Bani ji, ban gani kan ki yau gani
Ina farin cikin son ka shiya goya ni
Har dariya, murmushi kin ka sanya ni
Dama hakan nake so dakai nake maraba (dakai nake maraba)

Kisa a ranki kece
Ana batun ki sai gani
Nasan da zaki kare ni
Zaki rufa ki saye ni
Abin rabo ne
Don ina dake yasa bazan ga kowa ba (bazan ga kowa ba)

Dani da kai, alamar so
Abinda ke a rai feso
A zuciyata kayi naso
Kai zan kira na bawan so
Ka zo muje
Idan da kai bazan yi kuka ba
Kije dani duk inda zaki je
Mun shaku ne ba wanda zai raba mu

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель