Kishore Kumar Hits

Auta mg boy - Ga Sako текст песни

Исполнитель: Auta mg boy

альбом: SAIMA RANAR (Ep)


(AMG Boy Records)
Ga sako zo amsa ki aje mini shi
(Eh mana)
Ga sako aje mini, in zaki tafi
Nayi rubutu da tawada, farkon harafi
Duk sunan ki na zuba
Ba komai da ya raba
Kin sanya ni nayi gudu, har nayi gumi
Ciwon son ki ya bugan, duk nayi dumi
Soyayyah ta ja mini
Ba laifin da kikayi mini
Zallar son ki zan gwada, kowa ya gani
Ba zan ce ba zani ba, in zaki dani
Kinsan dai dake nake
Tarko naki ya rike
Ga hula saka mini, kaina ya rufa
Fifita kiyi mini, indai da zufa
Soyayyah farin ciki
Ta kau dan bakin ciki
In bake bazan yi bazan yi ba, nayi alkawari
Na dauka muje zuwa, nayi albishiri
Kece daya nake gani
Kin zo min a zamani
Kin sanyo farar tufa, wanka ya hadu
Mai kushe kabar fadi, don zaka kadu
Soyayyah da martaba
Ta sanya ina kiba
Duk bayan awa daya, ke zana kira
Murya taki inji ya, kin zam takwara
Bana son rabo dake
Rumfa taki zan fake
Ba kowa a zuciya, ke daya na rika
Bacin ran ki bani so, sanya a jaka
Ni hauka a so nake
Ba damar da zan sake
Nine naki kin sani, sam kar mu rabu
In ko har hakan ta zo, to zani tabu
Ba fata nakeyi ba
Ammah dai da fargaba
Karshen so idan yazo, toh aji jiki
Inko ribar sa ce tazo, toh ayi biki
Har ya'ya su habbaka
Wataran ko sai tsufa tazo maku, karshen lamari

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель