Kishore Kumar Hits

Hamisu Breaker - Dan dako текст песни

Исполнитель: Hamisu Breaker

альбом: Alkhairi


Kida

Lokacin da ina dako
Rayuwa ta dan rako
Ko wahala tai min jiko
Farin ciki ban san shi ba
Hana rantsuwa na tino
Rana guda naji dandano
Randa nai baban gamo
Labarin nake so in gino
Ranar ina bakin aiki
Sai naga wata tayo birki
Abinda ya ban mamaki
Sai ta ce, "Malam taso"
Aiki nake so in biya
A yanayin ta da tarbiya
Ina zatonta da kyan ainiya
Amman fara ce bakar niyya
Ban samu abinci ba ko daya
Ku bini a sanu a sanu
Don jin taya ta kasance
Na dauki kayan amma
Ban kai ba sai da maraice
Gidan su da nissa na sha
Wuya a takaice
Sai ta gaya mini cewa
Dan dakata karka zarce
Sai da na kai kayan duk tai tambayan sunana
Ko da taurin kaina sai nace ki bani kudina
Ka na ta ce, "Number na zan bata don wata rana"
Kash na ce, "Ina gabas kina yamma"
Dan Allah sallame ni da himma
Kinga na gaji sosai ga jikina ya dau kirma
Ta ce dani, "In yi hakuri in ci abinci kan in koma"
Sai na ce, "Na gode ina zaune nai ta tinani"
Shin wanan wacece? Zata zo haka nan ta tare ni
Bayan na kammala cin abinci tayi mini kyauta mai girma
Ta bani har number don kirata in na koma
Aiko ina komawa sai na kirata don mata godiya
Sai ta amsa wayata na fara zance tanai mini dariya
Ai ko nai ta yabata don zatona shine godiya
A hankali munyi sabo amma akwai wata matsala babba
Gidansu basa sona da cin mutunci bazan jure ba
To ku biyo ni a sannu ba anan kizo yai sakar ba
Dan na fara tinanin rubuta waka in rerawa
Lokaci baza yabar ni in bayyana labarin nan duk ba
Sai ku biyo ni a sannu
Sai da kai
Midget Mix
Kida

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Ole

2022 · сингл

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель