Kishore Kumar Hits

Hamisu Breaker - Ki bani dama текст песни

Исполнитель: Hamisu Breaker

альбом: Alkhairi


Ki bani dama-dama
Zanyi fama

Beat Amjad record
Idan ina tina kai na, ke na tino
Kanki nai damarata ko nazo na dano
Haba ki gane nufina ki yafe ni
Kar ki barni a zauce ki amsa wani
Kauna da sanki a rai sun taru
Karki bari sanadin kin kwaru

Har abada ni dake na saba
Batun in guje ki kin gani ba zan iya ba
Ko nazama naki zuciyata ki karba
Ki tai abunda kika so ni bazan hana ba
Nai miki magiya nasan nai kuskure
Ki mini afuwa sakar so ki warware
Ki mini lamunin zama ko wani bangare
Da zai shafi rayuwanki ya zam na tare
Na dada ambatonki na samu farar zuma
Tun daga kyan sufarki sai in dada kidima
Tilas ne in biki kana inyi lalanma
Ni banso ki furta kalmar sai anjima
Ki yafe ni sahiba
Kin zamto abun yaba
In ba ke nima nasan bazan iya ba
Makuli na zuciyata na baki
Kin kulle ki yadashi a tafki
San ranki
Ni dai magiya nake ki bude baki
Ki ce, "Kin hakurta babu fushi a ranki"
Nai laifi gare ki kuma na amsa da kai na
Ki hakuri ki bani dama in wanke kai na
Wani irin radadadin zafi a raina
Da na motsa sai dai in samo guri in tsuguna
Idan na nufo ki zana zo shin wa zai tare ni
Kowa ya ce, "In dakata sai dai a kashe ni"
Kuma kina fushi dani
Ina tinani taya zana karaso gunki kina tare ni
Dan aikinki ne, ke ko kin manta ni ne?
Mai hana damuwarki bansan ko sufone
Ban dama inzo gareki ko tankene
Tinanin kwakwalwa sirrin zuci ne
Nifa a kan ki ba nawa ko a tambaya
Komai nawa naki ne kinji habibiya
Jinina da naki sun gama zagaya
Mini jiki abun guda ne zinariya
Mai sona ki bani dama
(Ki bani dama-dama)
Idan kika bar ni zanyi fama (zanyi fama)
Ga sanki a zuciya yayi girma (girma)

Midget Mix

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Ole

2022 · сингл

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель