Kishore Kumar Hits

Nazir M. Ahmad - Wani Gari текст песни

Исполнитель: Nazir M. Ahmad

альбом: Wani Gari


Wani gari
Wani gari
Wani garin da ake kurba man gyada zalla
Wani gari
Bai kai gabas ga nisa ba
Wani gari
Bai canja a suna ba
Wani gari
Bai kai arewa hali ba
Wani garin da ake kurba man gyada zalla

Wani garin da ake kurba man gyada zalla
A wani garin sun tashi basu cin tata
Duk ayukan su sai ilimin ka, ka kyauta
A wani gari rana take bidar danta
Cikin sarautun su ko basu duba kankanta
A wani gari nema yakan zama sata
Suna da gona kuma basu kyauta noman ta
A wani gari mata suke fita tsinta
Tunda masu kudi basu san su dan kyauta
Wani gari ne ba dan isa da kudi ba
Wani gari ne ba a san fita da kaya ba
Wani gari ne basu fidda kai da zakka ba
Wani gari ake kurba man gyada zalla
Wani gari
Bai kai gabas ga nisa ba
Wani gari
Bai canja a suna ba
Wani gari
Bai kai arewa hali ba
Wani garin da ake kurba man gyada zalla
Rayuwar wani attajiri na dauko
Rayuwar wani hamshiki yau na leko
Akwai kudi sai dai masu saka mutum tarko
Dan ko ya tara ba shi cinsu yai tarko
'Kwai ilimi ga 'ya'ya gare a duk sako
Duk inda yaje aure yake kamar mako
Matan sa shidda ne kaga ya wuce iya kako
Jahili ne gashi ba sani furen sobo
Wani gari zai aure sai ya bar 'ya'ya
A wani gari
Zai tara dan karen kaya
A wani gari
Zai so magi ya bar saura
A wani gari
Mai binna dukiya zalla
Wani gari
Bai kai gabas ga nisa ba
Wani gari
Bai canja a suna ba
Wani gari
Bai kai arewa hali ba
Wani garin da ake kurba man gyada zalla
Ana kwana ana kwana ana tashi (toh fah!)
Yana tare da 'ya'yan da suka ki tashi (umm-umm)
Suna san su fantama da dukiyar shi (umm-umm)
A cikin 'ya'yan da akwai guda daban shi (umm)
Yana nan yana nan yana karatun shi (umm)
Yana nan da ilimi da hankali na shi (umm)
In mutunen ya karkace sai ya jawo shi (umm)
Yana bashi tallafi cikin karatun shi (umm)
Amman mutumin baza shi karba ba
Ba zai zamo a cikin masu fidda zakka ba
Ba zaiyi komai domin ya gyara bauta ba
Muten gari baza ma su more komai ba
Wani gari
Bai kai gabas ga nisa ba
Wani gari
Bai canja a suna ba
Wani gari
Bai kai arewa hali ba
Wani garin da ake kurba man gyada zalla
Bari kuji, bari kuji, bari kuji, bari kuji Allahuma
Da'da mai tarbiya da dadi (umhum)
Koda duniya da zafi (tabbas)
Neman lahira da dadi
Koda tai hadi da kaifi
Bari kuji, bari kuji, bari kuji, bari kuji Allahuma
Rana ta fito da zafi
Malam ta raba duniya da kudi (ah-ah)
'Ya'yen nasa sun ka zauna
Sunyi shawara ta zauna
Akan kawar da shi daga duniyar
Ko zasu zauna akan dukiyar sa
Bukatun su suka auna
Domin mutum ne shi ba dai isa da kudi
Wani gari
Bai kai gabas ga nisa ba
Wani gari
Bai canja a suna ba
Wani gari
Bai kai arewa hali ba
Wani garin da ake kurba man gyada zalla
Sun kar shi an shiga uku sun kar shi
Sun kar shi an shiga uku sun kar shi
Ba mutuwar sa ba akwai wani harsashi
Mata shidda ya da'da a iyakar shi
Ga kowa yana bukatar dukiyar shi
Daman baya basu yunwa a gidan shi
Ga kagara kaga duk sun hau nishi
Kowa yana kiran shi ne dan shi
Shi ne dan shi, shi sai an bashi
Ya tara dukiya zalla
Aure yake ya bar 'ya'ya
Ya binne dukiya zalla
Sun kar shi
Sun kar shi
Sun kar shi
Ah-ah-ah-ah, mun shiga uku sun kar shi

Ayi adalci
Ayi adalci
Ayi adalci

Allah yasa mu dace
Allah shi bamu ikon gyara ibadun mu

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель