Nayi nadama, masoyi haa Ni mata na aure na bida Na duba banganta ba ♪ Assalam salama farko nayi miki yan mata Don nayi shiri na da zato za kiyi mini gata Kauna harda so naki kiban raina ki faranta Karfin halin ka ashe (iyyeh) ya zarce a misalta Ka tuno abinda kayi mini a baya naki na manta Kace da iyaye na zaka zo ka kashe wayar ka Afuwar ki nake nema Lalala ba zan yi ma ba Na canza hali na A'a bazan aminta da kai ba ♪ Mun dace a soyayyah, ni dake in kin duba Hadin mu yayo dai-dai in an ganmu ba'a kushe ba Yarje mana muyo aure zuriyar mu ba zasu ki kyau ba Hmm umm, ka makara kalaman naka ba zasu shigan ba Ka dade kana bina da kalmar so naki na karba Sai a karshe na yarda, ka guje kasa nayi kuka Afuwar ki nake nema Lalala ba zan yi ma ba Na canza hali na A'a bazan aminta da kai ba ♪ Gaskiya doki na, na hayo gani gaban ki Yardar ki nake nema, a gida ku na mika sadaki Ko a hali zamuyi daidai nasan akwai ki da kirki Wallahi ka cuce ni, ka tsaya ni nayi maka burki Yaudara halin ka da kowa ya sani babu mamaki Yanzu ka juyo kaina kuma na zarce sanin ka Afuwar ki nake nema Lalala ba zan yi ma ba Na canza hali na A'a bazan aminta da kai ba ♪ Ni na tafi, na tafi, na tafi a baya yanzu na dawo Da so na hakika na zo gani kiyi mini oyoyo Kiran ki nake daure ki tsaya fuskarki kidan juyo Indai wannan ce dubarar taka jeka ka sauyo Na gane wannan dama ance namiji ba dan goyo Farin ciki idan nice fari kasa kuka Afuwar ki nake nema Lalala ba zan yi ma ba Na canza hali na A'a bazan aminta da kai ba ♪ Kiyi mini kallon so na idanu Ko a fuska a kayo dubi munyi kamannu Mai jirar so a fadar ki lallai zaya zaunu Kokarin ka nake kallo saurayi sannu-sannu Ganga bakin ki da zaki lallai zaki maganu Ka iya tsari ammah a kaina ba zakayi tasiri ba Afuwar ki nake nema Lalala ba zan yi ma ba Na canza hali na A'a bazan aminta da kai ba Nayi nadama, masoyi haa Ni mata na aure na bida Na duba banganta ba