Kayali sakar zuciya akan ki ni banyo ba Don na yarda dake kiyi mini soyayya kan gaskiya Kayali sakar zuciya akan ka ni banyo ba Don na yarda dakai kayi mani soyayya kan gaskiya ♪ Tun asalin soyayya ce ni dake muka kullo Da gasar faranta wa juna kamar a filin kwallo Ko ina kika zauna baki boyo don haske zai bullo Shi kyan hali jari ne, a gare ki sai dai koyo ♪ Komai ka gani daga Allah, na sani shine ya nufe ni In na gode yayi mani kari, har ace sam baya kamar ni Dace da masoyi dadi, shi yake da wuya zamani Tunda na samu zan nuna sam ba zancen yin boyo Kayali sakar zuciya akan ki ni banyo ba Don na yarda dakai kayi mani soyayya kan gaskiya Rikon tuta sai jarumi ba'a baiwa rago mai tsoro Wanda zaya tsaya ayi daga-daga a filin taro Tunda kin ban soyayyar ki zani boye shi a soro Duk wanda ya rabe ta komai nayi masa shi ya janyo Kayali sakar zuciya akan ka ni banyo ba Don na yarda dake kiyi mani soyayya kan gaskiya ♪ Kayali sakar zuciya akan ki ni banyo ba Don na yarda dake kiyi mini soyayya kan gaskiya Gani ya kore ji, reza an santa da kaifi Dubara ce ya hana, gani gurin mai kamun kifi Ita ko soyayya da anzo gareta nan a tsaya haka yafi Kalaman soyayya a gurin ka nake yin koyo Kayali sakar zuciya akan ki ni banyo ba Don na yarda dakai kayi mani soyayya kan gaskiya Ki daina zugani sarauniya zantukan bakin ki da dadi Dawisu ado ga kwalliya sannan kuma bakya kaudi Kamshi na turaren ki safamin dashi nayi fadi Ko'a hanya in naji sunan ki tukwici dole nayo Kayali sakar zuciya akan ka ni banyo ba Don na yarda dake kiyi mani soyayya kan gaskiya Da yabo zaki kake ba maza a gaban ka sun ja baya Komai ka nufa sai ka gan shi tunda nasan baka sanya Addu'a zan bika dashi koda yaushe don soyayya Yanzu kowa ya shaida ni da kai sa'a mukayo Kayali sakar zuciya akan ki ni banyo ba Don na yarda dake kiyi min soyayya kan gaskiya Kayali sakar zuciya akan ka ni banyo ba