A cikin halwar soyayya nayi gamo, gamo mai alkhairi A cikin halwar soyayya nayi gamo, da hasken annuri ♪ Juma'ar da za tayi kyawo, tun daga labara ake iya gane ta Tun farkon haduwar na gane, kunci zuciya zaki wanke ta Domin natsuwa da kamalar ki, na gane a cikin su kin bambanta Rabbi shi ya hada mu cikin kauna, ni da kai a sannu muka daidaita Halayya ta da naka sukayi arba, sun zamo daya ba mai nufin cuta Godiya ga rabbi kawai zanyi, da ya bani kai yayi min kyuta A cikin halwar soyayya nayi gamo, gamo mai alkhairi A cikin halwar soyayya nayi gamo, da hasken annuri Auren mu na so in an kai daurawa Sabuwar rayuwa mu komawa Ayyukan gida zamu tarawa Mu raba kowa yayi kamawa In na nemo abinci na kawowa Keko aikin kine kiyi girkawa Tambura idan nayi dokawa Wajibin ka waka rerawa Da kalaman nan naka da dada Masu sanyaya rai yayi kwantawa Bakin jiki sutura in ka sanyawa Mata in sun ganka dole suyi kyasawa A cikin halwar soyayya nayi gamo, gamo mai alkhairi A cikin halwar soyayya nayi gamo, da hasken annuri ♪ Ba a bada rikon soyayya, wanda yayi banga dalili ba Bada amana akan yarda ne, wanda yaci baiyi halacci ba Tausayi silar soyayya, mara shi bazai yi mutunci ba Gaskiya take sa ayi karko, koda hassada ba za'a rushe ba Sammakon da nayi a soyayya, na tabbata banyi ta a iska ba Nayi azarbabi wasu ke cewa, har yanzu banyi gamo da illa ba A cikin halwar soyayya nayi gamo, gamo mai alkhairi A cikin halwar soyayya nayi gamo, da hasken annuri Nayi gamo, gamo mai alkhairi