A dandali samari mun fito Yan mata muma mun fito ♪ Samari a dandali muna yin wasa Muda yan mata al'adar Hausa mai burgewa 'Yan mata a dandali muna yin wasa Da 'yan samari al'adar Hausa mai burgewa ♪ Sallama nayi da fari zani bude fili Tunda dai ni na saba yin hakan tun asali 'Yar budurwa ta naga fuskar ki na kyalli Kin hade tsaf kin cinye duka filin wasa Yan mata a dandali muna yin wasa Muda yan mata al'adar Hausa mai burgewa Komai kake so dole ne yama kyan kallo Duk bakin sa kace wata ya bullo Kunga nawa ai dole nayi wa saura gwalo Dandali ne sam baya shi a filin wasa Samari a dandali muna yin wasa Da 'yan samari al'adar Hausa mai burgewa Zuciyata fari take cikin ta da haske Don ko a cikin ta ba wata ya mace sai ke Zan bajinta kowanne iri domin ke Babu kowa idan dake a filin wasa 'Yan mata a dandali muna yin wasa Muda yan mata al'adar Hausa mai burgewa Kai da kaya abarsu kan wuya zai dauka Na amince ace dani na zam matar ka Zanyi doka ga wacce za tayo rabar ka Bani bata dani da ita sai sa'insa Samari a dandali muna yin wasa Muda 'yan mata al'adar Hausa mai burgewa ♪ Yan mata a dandali muna yin wasa Da yan samari al'adar Hausa mai burgewa Cikin samarin nan dake karkaran nan nikam Nafi kowa gayu ki so ni ayi miki barka Ko'ina kika wuce ayi miki sam barka A ce dake kin more cikin garin mu ki haska Lallai ka fiye raini tukunna wa zai so ka A haka nan tsami gaye wanda baya wanka Na wuce in soka Nemi dai tsarar ka Saurayina in yaji ka nikam zai chasa Samari a dandali muna yin wasa Muda yan mata al'adar Hausa mai burgewa A cikin dandalin nan na hange dan saurayi Zuciyata ta kama son shi wai ya za nayi Dauriya zakiyi fada mini kawai zakiyi Kuma in naji amsar ki dole sai gobe Babu saita a kanka kauce gurin wasa Nafi karfin in soka koda cikin wasa Wanda nake nufi cikin ku ya wuce wasa Idanuwa na a yanzu ma suna kallon sa Samari a dandali muna yin wasa Muda 'yan mata al'adar Hausa mai burgewa 'Yan mata a dandali muna yin wasa Da 'yan samari al'adar Hausa mai burgewa