Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Aure Na текст песни

Исполнитель: Umar M. Shareef

альбом: Babbar Yarinya


Na sa a rai aure na sai dake yanmata
Tunda kin amince min zuciyata babu sauran kuka
Na sa a rai aure na sai da kai dan gata
Tunda ka amince min zuciyata babu sauran kuka

Bazan manta ran da idanuna sukaiyo gamo ba
Bazan mance farkon haduwar zancen ki da kunnuwa na ba
Ranar da kika sace zuciyata ba zana manta ba
Nasa cikin kundin tarihi zan fadawa ya'ya na
Na sa a rai aure na sai da kai dan gata
Tunda kin amince min zuciyata babu sauran kuka
Dama an fadi rabon kwado bai hawa sama ya zauna
Koda ya haye tilas ne ya fado a kasa su gana
Matar mutum kabarin sa ko yana Nigeria ita ko Ghana
A sannu-sannu zaya zo su hade a kulla auren sunnah
Na sa a rai aure na sai da ke yanmata
Tunda ka amince min zuciyata babu sauran kuka
Soyayyah na kulle dakin ta a kan ki na tsaya
Bana so a san ma kofar ta, daga nesa a tsaya
Ni da kaina nake yin gadin ta, na riko kibiya
Sannan ban hada ki da kowa ranki banso yayo kuna
Na sa a rai aure na sai da kai dan gata
Tunda ka amince min zuciyata babu sauran kuka

Na sa a rai aure na sai dake yanmata
Tunda kin amince min zuciyata babu sauran kuka
Dadi na soyayyah za'a fadi ba'a zarce ni ba
Koda nida kai nace na fadi ba za'a karyata ba
Idanun ku suma shaida ne ban san wuya ba
Kaine ka saka ni cikin yanayi bazan so fita ba jigo na

Dole mu gode Allah sarki da yayi nufin haduwar mu
Arziki talauci shike yi ga wanda ya so cikin mu
Ku muyi mar biyayya komai muke so shi zai bamu
Sannan mu dau hakuri zamu ci riba dare koko rana

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Bako

2017 · альбом

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель