Bako Bako Bako Bako Bako Bako Sallama mutumcin bako ne Tunda nayi ku amsa min mutane Sunana Umar M. Shareef nine Mai kida da wakar Hausa ne Garin Kaduna aka haife ni hakkun ne Gashi na barta kan dalili ne Bako Bako Bako Bako Bako ♪ Na fito cikin gida watarana Zani je studio ma'aikata na Tafiya nake na rike jita na Sai na jiyo ana kiran suna na Wai budurwa ce ta baya na Sai na tsaya tazo har gaba na Tace dani nagode Allah na Yau ya nunan mawaki na Gari-gari na zo don mu gana Kwana uku nayi ta yawo cikin rana Sai tace mini 'Ka bani lamar waya, in koma gida na cika burina' ♪ Bako Bako Bako Bako Bako Bako Ashe, ashe a gida bata sanar ba Ba tace dasu zata zo gurina ba Neman ta ake ba inda ba'a je ba Sai gun aminiyar ta wacce suka saba Tace da ita Kaduna zata je Habiba Ita dai M. Shareef take duba Sai suka dauki motar gida babba Su kazo Kaduna suka zo duba Yan sanda dare rana Kullum dasu ake ta nema na ♪ Na baro asalin mahaifa ta Iyaye, yayye da kanni na Masoya masu goya baya na Nasan suna nan da kewa na Gani garin da babu dangi na Nasan da zasu share hawaye na ♪ Bako Bako Bako Bako Bako Bako Taimako a yanzun nake nema Wai shin wa zai yi mini alfarma? Ya bani koda makwanci ma Bana batun cin abinci ma Nabar wa Allahu mai girma Lamura na shi yasan dama Gaskiya fito da ita yan gulma Su gane banyi laifin ba mai girma Wayyo ina, wai yaushe zan koma? Hmm hmm yaushe zan koma? Nabar Iyaye, yayye, kanne wayyo masoya na