Duk wanda ke nema bazai ki samu ba Shi rago a barshi a baya ba zaya jure ba Rike Allah da Rasulu ba zaka tabe ba Taho ka gwada, komai ka bida, bazai ki yi ma ba Na sha wahala, kan so nayi kwalla, a baya nayi fama Nayi juriya addu'a kullum cikin sallah Da nayi hakuri, ya amsa mini na daina yin kwalla Sarauniyar mata Na samu mai kwantar min da zuciyata Na baki kaina ki rike ♪ Kin sauya zuciya tawa tayi sabun ta Cikin dubun masoya na kin ka bambanta Kin dau amanar ki hannuna kika damka ta Kuma zan rike ta da sirri zana boye ta Kin yantar dani Nazam mai gani A so na samu gari Kece magani Kin warkar dani Dadi cikin yanayi Sarauniyar mata Na samu mai kwantar min da zuciyata Na baki kaina ki rike ♪ Kyakkyawa, kyawun ki ido shi yaban labari Tattausar muryar ki kunni ke sanar mini zahiri Da kamshin ki zan fitar dake cikin dubun ayari Hasken farin wata, baya boyuwa sararin samaniya ♪ A baya na zama mai yawaita hargagi Saboda na tsinci kaina cikin sagagi Zuwan ki har bacci nake da magagi Kin fitar dani zafin ruwan cikin kogi Kin shayar dani zuma da madi da baya karewa Zan so ki sani, zan saka miki ba zaki koka ba (haa-haa)