Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Makaranta текст песни

Исполнитель: Umar M. Shareef

альбом: Kalaman Bakina


A makarantan nan duba ni na zama tauraro
A zahiri ban daukan raini kar nayi juyayi
Tayi ana yin shi a tsada ko kuma sari
Karfin hannu kar ya tabo garwashi zai kona shi

Idanuwa na sunyo hangen yan mata na tako
Da dai, da dai-da ba jin tsoro sam-sam basa shakko
Akwai guda dai a cikin matan mai halin yan tsirko
Tana kira na kullum a waya bana amsawa
Ta tura sakon text a waya ta sai nayi gogewa
Ammah cikin makaranta shan kamshi kullum ne aikin ta

Aji idan ya mace ta ja wannan ai dashi aka santa
Ta kare mutuncin kanta kar yan yara-yara su biyo ta
Ta canja fuska in taga alamun wajen ba tsaranta
Ka nuna missed call a gani domin a gane ita ke kiran ka
Ya zama shaida daga ranar ya zamo ka yanke son ka
Jan aji zai kare nasan kowa zai gane ta

Fadi na furta a tsakanin babba da yaro ke jan raini
Nayi mata nisa ammah so take sai ta kamo ni
In takaice zance na wuce da sanin ki a zamani
Yan mata na gyaran zama da ido in sun ganni
Shi abin sa'a ne bai guje wataran zaiyi dace
Watakila na karba, watakila sai na tantance
Tayi ana yin shi a tsada ko kuma sari
Karfin hannu kar ya tabo garwashi zai kona shi

A makarantan nan duba ni na zama tauraro
A zahiri ban daukan raini kar nayi juyayi
Abu mai kyawo na sai da kanshi ko ba talla
Ruwa ba'ayi masa hanya ko'ina yaso zai bulla
Dawisu idan ta fito tilas ne kowa zai kalla
Idan anayin zancen ka, ka kai ka gode Allah
Komai nake yi ido yana kaina Masha Allah
A yanzu nasan na ci gari na kai labari

Iya baki, kama bakin ki kar kiyi min raini
Ka fadamin tilas na fada ma tunda kai ka tabo ni
Shikenan zani wuce kar kiyi kuskure ki biyo ni
Mota da jirgi hanya tasu ba zata hade ba
A makarantan nan duba ni na zama tauraro
A zahiri ban daukan raini kar nayi juyayi
Tayi ana yin shi a tsada ko kuma sari
Karfin hannu kar ya tabo garwashi zai kona shi

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель