Labarin soyayya Abinda ke raina shi zani furta Labarin soyayya Abinda ke raina Na gaya maka bazan iya ba Da ka hakura ka kyale ni Zaka sha wahala ne kawai Nace miki ki daina fadin haka Nasan zaki iya Ki kalli ido na Idan nayi, kema sai kiyi Labarin soyayya Abinda ke raina shi zani furta Labarin soyayya Abinda ke raina shi zani furta ♪ Ba shawara so yake yi ba in zai shige zuci Mazauni in ya samu a ciki yayi tayin bacci Ba'a fitar dashi ta karfi shi so mai sanya kunci Yanayi yakan sa mutum ya zamo kamar mai maraici ♪ Soyayyah da dadi, idan kayi dace Damuwar rai ta kore wa mai duk amance Tasa farin ciki Ta kau bakin ciki Ta sanya dariya Kadan daga aikin soyayya ♪ Na rike alkawari Kuma zan nuna a gari Da kai zanyo alfahari Ko a ina nayi kudiri Soyayyah nasan kulawa Har rai a dinga yin farantawa Shike sawa a dinga yin kewa In anka tuna da juna Ba abinda na rasa a soyayya Inda kai a daina ma batun jinya Kallon ka shi yasa ni jin kunya Da idanun ka mai kyau da tozali