Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Kace Madadi текст песни

Исполнитель: Umar M. Shareef

альбом: Kalaman Bakina


Numfashi fita yake, ba adadi
Rayuwa sai dashi ba madadi
Yau kece madadi
Ko ince sanadi
Yau kece madadi
Ko ince sanadi
In bake ba batun
Soyayya, zo muyo soyayyah ni dake
Soyayya, don ko shine sinadari na zaman aure
Soyayya, zo muyo soyayyah ni dake
Soyayya, don ko shine sinadari na zaman aure

Cikin zuciya tawa, tana yin bugawa
Ga dukkan alamu kaine kake yin tahowa

Cikin zuciya tawa, tana yin bugawa
Ga dukkan alamu kaine kake yin tahowa
Maza zo da sauri, muje shakatawa
Kaban so in baka, muyo adana
Gare ni komai kike bukata
Zan yi miki shi cikin hanzarta
Domin zuciyar ki in faranta
A aikace ko cikin bayani
Zuciya ka zagaye
Ko'ina ka mamaye
Zuciya ka zagaye
Ko'ina ka mamaye
In ba kai ba batun
Soyayya, zo muyo soyayyah ni da kai
Soyayya, don ko shine sinadari na zaman aure
Soyayya, zo muyo soyayyah ni da kai
Soyayya, don ko shine sinadari na zaman aure

Fadin gaskiya tare shi ake kira so
Tausayi da kyautatawa duk yana cikin so

Fadin gaskiya tare shi ake kira so
Tausayi da kyautatawa duk yana cikin so
Kowa yana da wacce yake so
Nidai ke nake so
Ke dai zani furtawa so so
Soyayya abar so
Zuciya ka zagaye
Ko'ina ka mamaye
Zuciya ka zagaye
Ko'ina ka mamaye
In ba kai ba batun
Soyayya, zo muyo soyayyah ni dake
Soyayya, don ko shine sinadari na zaman aure

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель