Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Kallo Daya текст песни

Исполнитель: Umar M. Shareef

альбом: Kalaman Bakina

Daga kallo daya na gane a soyayya mun dace
Akwai biduri auren mu dake don na shirya
Daga kallo daya na gane a soyayya mun dace
Akwai biduri auren mu dakai don na shirya

Na nema an bani wannan girma ne
Burin rai samun shi jindadi ne
Auren so sunnah shi aikin lada ne
Ni da ke akwai shi masu matsayi ne
Auren soyayya
Mu kayo niyya
Ba jayayya
Muka daidaita

Cancanta in an duba ba'a jira
Halayya da dabi'u naka na ankara
Nasan in munyo aure sai na shahara
Jindadi da walwala kauna za'ayi bara
Duk inda na tunkara
Bani da tsara
Komai na tara a soyayya
Daga kallo daya na gane a soyayya mun dace
Akwai biduri auren mu dake don na shirya

Daga kallo daya na gane a soyayya mun dace
Akwai biduri auren mu dakai don na shirya
Kin zama, kin zama tamkar zinare zani kula ki
Can ciki, can ciki karshe a cikin zuciyata za ni saka ki
Ban bari, ban bari, ban bari, ban yarje ba ko kuda kar ya taba ki
Don nayi yawo a kasashe
Ban yo gamo da irin kyakkyawan fuskar ki
Da iri na jiki
Lafuzan bakin ki
Su sani jiri

Zo mu zauna nayi ma maraba
Wuya da dadi bazan guje ba
Yan gulma da suka bazan biye ba
Duk wanda ya koce ka ya nemi gaba
Don ina kishi
Zan sanyo mashi
Ko harsashi in buge makiyi na
Daga kallo daya na gane a soyayya mun dace
Akwai biduri auren mu dake don na shirya

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель