Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Jini Da Fata текст песни

Исполнитель: Umar M. Shareef

альбом: Kalaman Bakina


Jini da fata
Ki zo mu zauna
Zafi rabuwar so karki tafi
Jini da fata
Zanso mu zauna
Zafi rabuwar so zamu tafi
Hmmm-mmmm
Munyo sabo soyayya ce mun kamu da juna
Farkon haduwarmu dake lokaci daya kin shiga raina
Nai mikki tayin So kin karba naji dadi a raina
Sam banda tunanin zamu rabe a dare ko rana
Yau zaki barni
Cikin tunani
Kama hannuna kice mu tafi
Hahahaaa
Babu zata soyayya
Ta shiga rai ban shirya
Duk nazari ta sauyaa
Idanu duk sun juya
Hayawe ke ta tsiyaya
Duk sanadin soyayyaa
Gashi zana juya
In kama hanya
So samuna da kai zana tafi
Tafiyarki bazata zamo shaidar munyi rabo ba
Da zanyi hakan zuciya ba za tai mun uzuri ba
Kece kika warkan cutar dā ban san magani ba
Makarantar So kalmar rabuwa bata karbu a nan ba
Zanzo gareki
Da batun aurenki
Zan biyo sahunki idan kin tafi
Hmm-mmmm-mmm
Ji nakeyi tamkar a mafarki ne ba zahiri ba
Dama a mafarki ne zan bude ido nai duba
Shakuwarmu da kai tamkar munyi shekaru mun saba
Ga zobe na ka rike in na tafi ka dinga duba
Sanya hannunka
Ka bani naka
Ya zamo tamkar alkawari abun nufi
Jini da fata
Ki zo mu zauna
Zafi rabuwar So karki tafi

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель