Fuskata ki kalli labarin zuciya Farin ciki soyayyar ki ta sanya Fuskata ka kalli labarin zuciya Farin ciki soyayyar ka ta sanya ♪ Ke na gani cikin bacci na kin iso Nayi hange daga nesa ki karaso Ga mazauni a gare ki nake yin iso Ke kadai ce a cikin mata nai ta so Gani gaki ai zan baki kisan da so A cikin raina kullum nake yin bacci ♪ Ai gani ya kore ji na gan shi a zahiri Na yarda dakai ko'a ina zanyo fahari Idan da akwai ka gu za'a ganni da hanzari Babu kunya zan saka nishadi rai yayi fari Da idanu in kalle ka cikin ayari Za na cafke ka kauna ce ta sanya Fuskata ki kalli labarin zuciya Farin ciki soyayyar ka ta sanya ♪ Ki yarda dani kan so zo mu tafi zan baki amana Sa ni a ranki komai zafi sam kar na fita Ka yarda dani kan so zo mu tafi zan baka amana Sa ni a ranka komai zafi sam kar na fita Nayi ajiyar so a cikin raina na kira shi da sirri Ko na fada maku ne sunanta hasken annuri Ta shiga raina komai zanyo sai da ita a tsari Karda ku bata mata idan bakwa so kuga tai kokawa ♪ Na kama dahir gani na Mai nuna kishi a kaina Idan iyaye sun furta sun kace in fito da miji na Lissafi ya kare kai wa kake ganin zan nuna Kaine ka zamto na daya je iyayen ka sai kai turowa Ki yarda dani kan so zo mu tafi zan baki amana Sa ni a ranka komai zafi sam kar na fita ♪ Burin zuciya ta samu masoyin gaskiya Burin zuciya ta samu masoyin gaskiya Burin zuciya ta samu masoyin gaskiya Wanda ya taki sa'a gurin Allah yayi godiya Gamo da katar nayo da sa'ar duba ina dariya Nasan bani shan wuya Na samu son gaskiya Na dace Harsashe kila wakala ne ba zai zama gaibu ba Fatan da nake zaman mu abadan da'iman ba farraku ba Kullum muyi ta cigaba Har karshen rayuwa a takaice