Burin zuciya ta samu masoyin gaskiya ta dace Burin zuciya ta samu masoyin gaskiya ta dace ♪ Burin zuciya ta samu masoyin gaskiya Wanda yayi taki sa'a gurin Allah yayi godiya Gamo da katar nayo da sa'ar duba ina dariya Nasan bani shan wuya Na samu son gaskiya na dace Harsashe kila wakala ne ba zai zama gaibu ba Fatan da nake zaman mu abadan ne ba farraku ba Kullum muyi ta cigaba Har karshen rayuwa a takaice Komai Allah ya nufa sai yayi ba mai hana shi Ni ke mun hadu kan soyayya ne cikin nufin shi A raba ni dake ba dai mutum ba sai shi da kanshi Hassada ko shi ba zaiyi min ba don na rike shi Maganin dukkanin cuta Na fadi kuma na nanata ki dauka Zantukan da kayo hakika ni shi zani dauka Shi ya dace dukkanin Musulmi kowa ya dauka Yarda Allah shine dai mai yi ka gujewa shirka Inda yaso dole kaje in yaki ko babu mai kaika Shi ya hada mu Don haka bamai raba mu (soyayya) ♪ Nishadin zuciyata kece mai share hawaye Zan shaida nafi son ka da kowa dangi har kawaye Kuka nake in na tuna akwai rabuwa mai sa hawaye Ko raina ne ya baci idan na tuno ka sai na janye Babu mai bata miki in barshi muddin ina a raye Kunyi min komai iyaye in kun bani shi ba hawaye na dace Burin zuciya ta samu masoyin gaskiya ta dace Burin zuciya ta samu masoyin gaskiya ta dace