Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Tsaya Kiji текст песни

Исполнитель: Umar M. Shareef

альбом: Kuyi Hakuri


Ni zan tafi bani so naji, kalma ta so kabar fada min
Karki tafi tsaya kiji, nazo da so karba rike min

Da so na kamu a zuciya
Ammah sai dai ina shan wuya
Nazam kamar mara lafiya
Kira ni bawa ke sarauniya
Wadan su za suyi dariya
In kika ce. "So bakiyi min"

Zana zamo mijin ki in kika yarda
Zan baki kula in sa ranki a randa
Masarautar so ce na gina miki fada
Bani ganin kowa sai ke idanuwa na kauda
Bara nakeyi ki shaida
Soyayya taimaka ki zuba min

Ita gaskiya ce guda daya
A hada ta da karya basu gauraya
Nasan dalilin ka na bibiya
Nasara tana ga mai gaskiya
Nayi maka nisa sam baka cim min

Ki bani dama in jarraba
Ki ce dani, "In wuce gaba"
Dana sani baza kiyi shi ba
Karda ki kaini mararraba
Dubi hawaye suna zuba
Amsar kice kadai zata tsayar min

Kiran da kake min, bazan ji shi ba-ba-ba
Dadin bakin bazai rude ni ba-ba-ba
Soyayya tace bazan baka ba-ba-ba
Zubar hawaye bai gamshe ni ba
Daga fatar baki soyayyah kake min

Ni zan tafi bani so naji, kalma ta so kabar fada min
Karki tafi tsaya kiji, nazo da so karba rike min

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель