Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Soyayya Ce текст песни

Исполнитель: Umar M. Shareef

альбом: Kuyi Hakuri


Soyayya ce, nayo dace
Da nayo kuka, yau ya kare
Soyayya ce, nayo dace
Masoyi bar kuka, ni zan share
Komai yayi mafari zaiyo karshe
Komai yayi tsauri zaya gushe
Wanda yake da jari zai sana'a ashe
Wanda ya shuka hakuri riba zai kwashe
Ni na jaraba
Yanzu ku duba
Ni naci riba
Kunci ya kare
Mai imani dole za'a jaraba shi
Har kan sa ya kulle ya kasa bude shi
In yayi hakuri a sannu zai ga sakamakon shi
Misali gani nan zan maye maka gurin shi
Zan sa kayi murna
Kar kayi kuna
Da kai zan zauna
Hawaye in share
Gani a duniya sabuwa rayuwa ta canza
Bani da damuwa ke kika zo kika min visa
Godiya da yawa baki na gare ki ya furza
Kyakkyawar masoyiya zuciya ke bata canza
Na daura baza
Rawa nayi girgiza
Ina yin shi da izza
Haushi na cire
Dani da kai zamu zam abin kwatance
Mata da miji haka babbar nasara ce
Idan da shaidu ayi komai a mutunce
Duk wanda bai so ya gani ransa ya bace
Mu mun dace
Da soyayyah ce
Mai riba ce
Karshen ta da aure
Soyayya ce, nayo dace
Da nayo kuka, yau ya kare
Soyayya ce, nayo dace
Masoyi bar kuka, ni zan share
Soyayya ce, nayo dace
Da nayo kuka, yau ya kare

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель