Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Mai Kaunata текст песни

Исполнитель: Umar M. Shareef

альбом: Kuyi Hakuri


Mai kauna ta ba wacce ta kai ki gare ni fannin so
Kece farko, karshe a labarina soyayya
Mai kauna ta ba wanda ya kai ka gare ni fannin so
Kaine farko, karshe a labarina soyayya

Mun girma, ni da ke a cikin so mun kayo sabo
Akwai dama, auren mu da ke ashe inda rai da rabo
Na soma mutuwa ta zamo rabuwar mu zo dibo
Ki daina fushi
Dukkan mai rai tilas yabar duniya
Mai kauna ta ba wanda ya kai ka gare ni fannin so
Nayi kuka domin watarana nasan sai mun rabe
Matar ka zan kare mutunci naka kar ya zube
Mai hauka ita zata rike shi a hannu har ya kadai
Fatana mu kasance tare a sabuwar duniya
Mai kauna ta ba wacce ta kai ki gare ni fannin so
Kece farko, karshe a labarina soyayya

Kaine kofar zuciyata duk wanda yazo kai zai iske
Don haka ba wani mai shigan ta sai ka bashi dama haka yake
Kaine mai mulkin ta, sarautar tawa kai ka rike
Tawa daban soyayya ta a gare ka gangariya

Tunda kin bani dama
Ba zanyi wasa dashi ba
A son ki zan zama kurma
Sukar ki bazan jiyo ba
Ba abinda zai sani nadama
Zabin ki banyi kuskure ba
In na dauko keke na kece zaki hau carrier
Mai kauna ta ba wanda ya kai ka gare ni fannin so
Kaine farko, karshe a labarina soyayya
Mai kauna ta ba wacce ta kai ki gare ni fannin so
Farko, karshe, labarin soyayya

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель