A yau take babbar rana Auren sunna na masoya Dangi da kawaye, abokai Ku zo muyi murna Na sa ubangiji na mai duniya Sarkin da shike mini lafiya Ya bani baiwa gata kun jiya Gare shi sai dai inyi godiya Alhamdulillah sarki daya Roko nake ka dadan juriya Waka ta auren so zan biya Sunnar ma'aiki mai juriya Manzon mu shi yayi gwagwarmaya Muke ta nunfashi duniya A yau wadan su suke kwaikwaya Miji da mata sun zama daya Farin ciki ya same ku yau Kuka na mage bai wuce miyau Zabin ki shine aka baki yau Idonki yayi haske yayii fayau Kisan yamo sai da kayau-kayau Cike da murna kike har wayau Duk wanda bai murna yayi baya Amarya kyakkyawa ce amarya Ku tambayo ango in nayi karya Tana da tarbiyya ita amarya Za tayi wa ango biyayya Waje na girki bata da sanya Mu tuka mota mata tukunya Mota ba taje ba in babu taya Gida babu gida in babu mata Mutum babu mutum in baida mata Da wancan da wancan sunan su mata Ammah akwai dai ta kera mata Akwai guda dai ta zarce mata Akwai guda dai ta kera mata Mai kyau na hali kuji manufata Mai yin biyayya a gurin miijin ta Wannan amarya ta cire tuta Ana fadar ta maza da mata Dukan su dangi suna yabon ta Suna fadin kyawawan halin ta Allah ya kawo ranar bikin ta Can za taje ta fara bauta Farin ciki yau ranar ku ce Kun zama daya ba cece-kuce Kamar da wasa yanzu taka ce An daura auren ku amarya ce Komai za tayi ma idan kace Kaima ka nuna mata halin kane Ana fadan kyan dabi'un kane Niko nace tayi sa'a ne Amarya kin dace miji amarya Yana da zance daya babu karya Yana da kyawu kuma ga wushirya Taho kayi mata fara'a amarya Taso ka taso ango Taso ka taso ango Taso amarya taso Taso amarya taso (Kema) A yau ina ta zumudi Auren sunna dadi Auren soyayya dadi Kuzo da takon fadi Sha zuma in kun so ku sha madi Ku muke wa sarauta muna nadi Da tambura na na buga ina kidi Ni Shareef Umar mai wakar gidan kidi