Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Rariya текст песни

Исполнитель: Umar M. Shareef

альбом: Masoya


Tankade da-da sai da rariya
Rariya-rariya
Rariya-rariya
Rariya-rariya
Tankade nayo na sa rariya
Kece kika zam tsaba zabi na a soyayya
Tankade nayo na sa rariya
Kai ne ka zamo tsaba zabi na a soyayya

Na takande soyayya ta na sa rariya-rariya
Dan in guji cuta Allah ne mai kariya-kariya
Kuma na dace dan na samo mai tarbiya-tarbiya
Lafazin ta da dadi sam-sam bata ashariya-ashariya
Nazam' gwanin so dolle ayi mini jiniya
In na taho kiyo dauki ki min tarba ta soyayya
Rariya-rariya

Nayi nisa a so nai kololuwa loluwa
Cikin kala damin nan nai yo tsuntuwa-tsuntuwa
Kai ka zamai mini allura na cikin ruwa, cikin ruwa
Nazama mai sa'a samun ka a rayuwa, rayuwa
Duniya ta yau ta dawo sabuwa
Kai ka shigo kayo aiki dolle in maka sakaya
Rariya-rariya

Ruwan sama in kaga yayi zubowa ai damina ce
Aure in kaga yai daurewa wannnan kauna ce
Cutar Allah na da yawa naga
Baiwa-baiwa ce
Shi ya hada mu dake kan aura an ce mun dace
Na rasa ki a soyayya sai na mace
Ko-ko jiki ya bar aiki tunda rabin shi ya tsaya
Rariya-rariya

A haggu da dama kai na gano kai
Na fada wa iyayye, "Kai ne zabi"
Littafin so ciki babi-babi
Sunan ka yana ciki fannin hubbi
Kowa kagani a cikin littafin gallery
Dolle hannun sa 'kwai mulki koko sarautar soyayya
Tankade nayo na sa rariya
Kece kika zam tsaba zabi na a soyayya

Tankade nayo na sa rariya
Kai ne ka zamo tsaba zabi na a soyayya
Tankade nayo na sa rariya
Kece kika zam tsaba zabi na a soyayya

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель