Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Ranar Farin Ciki текст песни

Исполнитель: Umar M. Shareef

альбом: Masoya


Ranar kuke jira yau gashi tazo
Nima da tambura na gani nazo
Ango nake yiwa shi da amarya
Miyo rawa ta murna anyi aure
Ranar kuke jira yau gashi tazo
Muma da tamburan mu gashi munzo
Ango muke yiwa shi da amarya
Miyo rawa ta murna anyi aure

Da fari na kira babban sarki
Shine yayo mutane da dawaki
Shi ya nufa nakai wanga mataki
Nayo fice cikin waka aiki
Nata godiya ga Allah babu birki
Inata yi a yau wasu na liki
Auren dakayo ne da sadaki
Hakan sun ganshi tamkar a mafarki
A yau amarya zata tafi daki
Ibada chan zaki
Ga ango kiyi kirki
Idan zakiyi girki
Ki kirga da hanunki
Abinda yafiso shi zaki girga ke amarya
Ranar kuke jira yau gashi tazo
Muma da tamburan mu gashi munzo
Ango muke yiwa shi da amarya
Miyo rawa ta murna anyi aure
Eh ranar da kuketa jira gata tazo
Dangi maza da mata duka sun zo
Wadansu yan Zariya wasu Gwarzo
Da ganin bikin ya wuce aci kanzo
Ga ruwan kudi na zuba sunyi tozo
Ango amarya dan ku kowa yazo
Farin ciki mu nuna babu gezo
Dan kwaliyyarku tai kyau tayi cizo
Da aure kuma raya sunnar manzo
Ni koh addu'a agareku na burzo
Dangi kuzo kuzo kuzo kuzo
Musha rawa mu tashe da amarya, amarya
Ranar kuke jira yau gashi tazo
Muma da tamburan mu gashi munzo
Ango muke yiwa shi da amarya
Miyo rawa ta murna anyi aure
Me yafi dadi ne a zaman tare amana
Amarya ango ya dace ku kare hakkin juna
Idan an zauna an saba tarihi haka ya nuna
Idan kun saba kuyi sulhu karda ku yarda ku nuna
Makiya masu so sugano ku a rana, rana
Kun tsole idansu kunji batuna, tuna
Allahu yakai mu watan wata rana, rana
Ku haifi diyanku kusa masa suna, suna
Allahu yasaka muku albarka
Dikanku dani danake waka
Iyaye nayin sam barka na doka kidana kun taka
Amarya taso
Eh ke ango ke so
Haba
Ranar kuke jira yau gashi tazo
Muma da tamburan mu gashi munzo
Ango muke yiwa shi da amarya
Miyo rawa ta murna anyi aure

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель