Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Ni Maraya Ne Bibki текст песни

Исполнитель: Umar M. Shareef

альбом: Masoya


Ni maraya ne
Ni maraya ne

Iye amarya soyayya ango kaima soyayya
Auren an daura dangi kowa na murna iye
Da sunan Allah sarki zana faro waka ta
Ahadun babban sarki kai ka kagi halitata
Kai kayo mu maza mata sanan kace muyi ma bauta
Aure na nan a ciki dangina fa mu inganta
Yau ga wasu sun shirya rabbi zasuyi ma bauta
Domin su na shirya ta
Zana rero wakata
Zanyi gyran murya ta uhm uhm idanyi nasiha ta
Amarya kyakkyawa sarauniya ce tayo kwaliyya
Ke kowa ke kallo yanata jiran takunki da dai daya
Iye amarya soyayya ango kaima soyayya
Auren an daura dangi kowa na murna iye
Taro nan yayai taro maza da mata duka sun taru
Ga iyaye ga yaye har kanne duka sun jeru
Ga abokai harda kawaye nata jiran mai zai faru
Kalaman bakina kowa ke yin sauraro
Fatan da nake zancen da zanyi kowa ya karu
Wasu sun dage da rawa wasu sun zauna a kujeru
Maza taso ango ga amarya kaine jigo
Babu kwanan shago tunda tasai ma bargo
Amarya soyayya ango kaima soyayya
Auren an daura dangi kowa na murna iye
Eh hakuri jari ne ango da amarya kunjiya
Hakuri riba ne ku gwada karshe kuci muriya
Hakuri tsani ne ku rike shi da karfi igiya
A zaman mu na duniya kar mu biyewa zuciya
Ku zauna lafiya dan Allah babu hayaniya
Dan wata rana zaku zamo iyaye bai daya
Ina da yakinin zakuyai wa 'ya'ya tarbiya
Ku tausasa zuciya dan Allah sai kuyi juriya
Sai kuyi juriya hakuri sai kuyo juriya
Amarya soyayya ango kaima soyayya
Auren an daura dangi kowa na murna iye
Kin dace da miji amarya zabin Allah ne
Tinda anyima shaidar shi mai tsoron Allah ne
Mai irin wanan hali ai zaya kare hakki ne
Nasan zai baki kulawa zai rike ki amana ne
A tsakanin juna ku zamo masu boye sirri ne
Naji anyo shaidar ki amarya ina dada jan kune
Naji ance zakayi ladabi da biyaya ga ango ne
Dan ance kin iya girki sanan ga tsabta ne
Kyauta daga Allah ne
Kyauta daga Allah ne
Amarya soyayya ango kaima soyayya
Auren an daura dangi kowa na murna iye

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель