Kyautar so na baki domin kin wuce aro Ni mai zaki bani? Allah sa nayi farin jini Kyautar so na baka komai na tattaro Allah sa zaka dauka yaro mai farin jini ♪ Sai murna nake a yau na cika buri Nayi gamo da sahiba mai kyan tsari Ta shiga zuciyata tasa annuri A fagen so ku dube na zarce gori Karaya akewa dori Murgi sai da mari Ya Allah tsare mu dukkanin sharri Soyayya muzam cikin masu sukuni ♪ Naga farin cikin dake sawa ayi kwalla Don a isar da sako ke sawa ayi shela Don ayi tarbiyya ake rike bulala Jirgin so na hau a yau sama na lula A garin so na bulla Soyayya na kulla Yau sai godiya nake a gurin Allah Don wannan farin ciki shi ya bani Kyautar so na baki domin kin wuce aro Ni mai zaki bani? Allah sa nayi farin jini ♪ Kyautar so na baka komai na tattaro Allah sa zaka dauka yaro mai farin jini Da wanda zaya ce miki ina, ina masoyin? Kafin ya rufe baki za a ganni na fito Don ke kadai na sa raina, bana yin bulayi Safiya zuwa rana ke na ambato A cikin raina kin aje hoto Da soyayyar ki bana yin koto Ko an daura son ki can sama na reto Ni zan takalo in hau ko ba tsani ♪ Soyayya ruwan zuma ce, nasha gani kwance Masoyi ya asirce ni bani yin gani Wallahi nayi dace nazam abin kwatance Sam bani bada rancen masoyi gani kun gani Ni da kai muka dace Da farar zuciya ce Masu bakin hali hanya tasu mun kauxe Allah ne ya yarda mun kece raini Kyautar so na baki domin kin wuce aro Ni mai zaki bani? Allah sa nayi farin jini Kyautar so na baka komai na tattaro Allah sa zaka dauka yaro mai farin jini Allah sa nayi farin jini