Hisabi shi nayi wa kaina akan so Makoma ta zamo da dadi (iyeh-iyeh) Hisabi shi nayi wa kaina akan so Makoma ta zamo da dadi (iyeh-iyeh) A kallo ke nake wa kallo in kara Kalami in kikayi batu dole a saurara Wajen kwalliya ko dukka mata sun sara Mukami babu wata sai ke Mafarki wataran yakan zama hakika Ka girba sai abinda kaine ka suka Alkhairi shi nake ta fata na saka Domin baya na ya zam da haske Akwai watarana ina jiran ta tazo Da zanga iyaye abokanai dandazo Ana raba goron daurin aure anka zo Sai walimar shinkafa da wake Hisabi shi nayi wa kaina akan so Makoma ta zamo da dadi (iyeh-iyeh) Hisabi shi nayi wa kaina akan so Makoma ta zamo da dadi (iyeh-iyeh) Mai nema karya fidda ran zaya samu Kamar ni, nasani akwai lokacin mu Idan rabbi yayi nufin sa tilas a barmu Da igiyar mahassada mu tsinke Ba canjin ra'ayi, a so kine dai nayi wa alkawari Duk zafin yanayi bani gudu indai kina a gari Ba nayin kwadayi wulakanci na guje fita hadari Halili gun nema na koke Kamanni mukayi da kai na duba haka Da halin mu iri daya ba farraka Ashe dole zaman mu zaiyi dadi haka Mu more muci duniya da tsinke Hisabi shi nayi wa kaina akan so Makoma ta zamo da dadi (iyeh-iyeh) Hisabi shi nayi wa kaina akan so Makoma ta zamo da dadi (iyeh-iyeh)