Bayan mutuwa bakomai daga kai sai halayyar ka Bayan mutuwa bakomai daga kai sai halayyar ka Da sunan Allah na daya Sarki mahaliccin duniya Kaine mai mulkin gaskiya Wanda sam baka yin murdiya Kai ka tsara mana duk rayuwa Muyo kuka ko muyi dariya Rokon da nake sarki daya Daura ni a hanyar gaskiya In bar aikata sabo, yazam bana yin zunubi ko daya Komai in kaso ni zan zamo, sam ba wani mai yin kariya Bukatu na duka na tattaro, nasan kaine zakayi biya Nazo neman tuba, laifukan sabo wanda nayo jiya Wanda nayo jiya, laifukan sabo da nayo jiya Ni abinda ya sani a damuwa idan na tuna ranar mutuwa Ranar da bawa zaya zam mai kishi yana neman ruwa Iyaye, ya'ya, ko yan'uwa, ba wani mai yi maka garkuwa Dukiya ko mulki ka rike, suna kallon mai ke faruwa Yansanda ko sojoji, sun zama hoto sannan kuwa Yanda Allahu yaso zaya yi, a wannan ranar da rayuwa Inka mutu ayi maka kuka, idanu suyi ta zuban ruwa Idanu suyi ta zuban ruwa, suyi ta zuban ruwa Duk soyayyar ka da dangi ranar ta kare a gare ka Bayan anyi maka waka, zaka ga ana ta saurin kaika Yan'uwa abokan arzki zasu kaika cikin kabarin ka A sanya ice a saman ka, sannan kasa ta biyo bayan ka Wadan da suke kaunar ka su zasu yo addu'a a gare ka Su juya suyi tafiyar su, a cikin kabarin ka su barka Daga nan sai halayyar ka, ina kayi mai kyau jindadin ka In kayi mara kyau halin ka, rannan ba mai kwacen ka Ba mai ceton ka, ranan ba mai ceton ka Kabari ranan ganina dashi na kasa bacci Gabana sai faduwa yake, na kasa cin abinci Ba zama ciki ba'a juyi, kwanciyar ciki irin na bacci Tsawo, fadi daidai da kai babu kari domin karamci Sannan ba hanyar iska da zata zo maka kamar mafici A cikin kabari da bayani ba ankai ka bane kayi barci Mala'iku zasu zo da su'ali, tambayoyi babu ragwanci Ba sani kuma ba sabo, in kayi daidai ka samu karamci In ka saba Allah a duniya daga nan ka fada kunci Ka fada kunci, daga nan ka fada kunci Yan'uwan ka sun manta ka, basa tuna ka a rayuwa Aiyukan da kayo masu kyau, su zasu zame maka garkuwa Da su za'a dinga tuna ka, jindadi ne gun yan'uwa Har a dinga yi maka addu'a, sunan ka baza'ayi mantuwa Wanda yayi aiki mara kyau mutuwar sa ba mai damuwa Kaji wadansu na ta fadi an rage mugun iri a rayuwa Ina amfanin mummunan shaida duba mini yan'uwa Allah taimkaa mini, lahira kar in shiga damuwa Kar in shiga damuwa, lahira kar in shiga damuwa Idanu na ta hawaye na tuna ran tsayuwa a gaban gwani Ranar tonon silili komai ka aikata sai ka gani Sharri ko alkhairi ranan mutane duk sai sun gani Sirrin da kayo shi cikin duhu (ranar jama'a sai sun gani) Malaman da suke rufe gaskiya (ranar jama'a sai sun gani) Da watan azumi ka sha ruwa (ranar jama'a sai sun gani) Kai asiri ka kashe dan'uwa (ranar jama'a sai sun gani) Ka cinye hakkin marayu (ranar jama'a sai sun gani) Mai tauye mudi gun awo (ranar jama'a sai sun gani) Ga zina anyi ta a boye (ranar jama'a sai sun gani) In fashi da makami shi kayi (ranar jama'a sai sun gani) Idan fashi da makami shi kayi (ranar jama'a sai sun gani) Maza da suke neman maza (ranar jama'a sai sun gani) Mata da suke neman mata (ranar jama'a sai sun gani) Ka kashe rai kuma ka sha jini (ranar jama'a sai sun gani) Anyo zabe kayi murdiya (ranar jama'a sai sun gani) Mai shirka baka da gaskiya (ranar jama'a sai sun gani) Shirka babban sabo ne dubiya (ranar jama'a sai sun gani) Mace mai daga sauti kan miji (ranar jama'a sai sun gani) Wata ta fita babu sanin miji (ranar jama'a sai sun gani) Kudin cefane wata ta rage (ranar jama'a sai sun gani) Mace mai cutar da kishiya (ranar jama'a sai sun gani) Ta bada kanta ga boka (ranar jama'a sai sun gani) Tasa magani a abinci (ranar jama'a sai sun gani) Um, wayyo Allah (ranar jama'a sai sun gani) Wayyo Allah yau tuba nake (ranar jama'a sai sun gani) Ni Umar tuba nake Allah