Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Ba Zato Ba Tsammani текст песни

Исполнитель: Umar M. Shareef

альбом: Masoya


Kauna ba zato ba tsammani ta shige cikin raina
Kai nake wa tayin so amshi kace kana so na

Babu zato ba tsammani furucin ki kamar cikin barci
Ni da ke ba zancen so sharadin ki bai kau ba

Asalin soyayyah kai na saka cikin zuci
Ina fara tunani naka sai na kasa yin bacci
In ka ambaci ya mace sai inji ni ina cikin kunci
Zo ka bani ruwa na zuma karka bani mai daci
Kai nayi wa tanadin soyayyah
Karka barni inyo jinya
Riga ta sonka ne na sanya dubi jiki na tayi mini dai-dai

Kece kika ce mini kalmar so kar na furta yanmata
Inko na kuskura nayo haka zaki tsane ni mun bata
Niko da bani son haka nayi na'am na kira ki kanwa ta
Nayi nisa a son wata ni a gani na zamu dai-dai ta
Son ta nayo bata
Hankali na ya karkata
In bata zan haukata dani da ita hadin mu yayi dai-dai

Yau na bayyana ban boye ba cibi ina wanka
Zancen dake cikina na fiddo fili ya sha iska
Ka mamaye ni ka shiga raina babu shiri ina binka
Karda kace dani baka so na zai saka ni nayi kuka
Amshi makulli na ka tuka
Ko'ina kace dani taka
Kowa ya kira ni matar ka
Zan amsa sunan hakan nidai

Wacce nake so da soyayyah
Na sani tana a kan hanya
Zana nuna miki da gayya
Aure na da ita na shirya
Dube ta nan haka kiyi dubawa, madubi duba
Da ita dani mun saba, ba zamu rabe ba
Handa ta jini a soyayyah, ba za'a raba ba
Fuskar dake ciki ne zabi na rike ni muje dai-dai

Na rude jindadi ka bani kauna
Nagode, nagode ka ceci raina
Kawo hannun ki nasa zobe na alkawarina
Tun haduwar mu a farko so tarkon ki ya kama kauna
Nayi haka, nayi haka, na nuna bazan boye ba
Nima nayi haka, nayi haka na nuna ka ba jin kunya ba

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель