Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Zumu Zauna текст песни

Исполнитель: Umar M. Shareef

альбом: Tsintuwa


Zo mu zauna da dake masoyiya
Na amince da ke har zuciya
Aure ni dake na shirya
Amana zan rike ba gajiya
Tunda kin mini so da gaskiya
Don haka ban barin ki sha wuya
Zana kula dake zinariya
Na ji dadi wa zai mini barka
Nayi godiya a gare ka
Tunda ka kira ni matar ka
Zana baka duka hakin ka
Ni, ni ban yarda ba a kushe ka
Na yaba da halin ka
Saboda iya takun ka
Natsuwar ka, jarin ka, ni na so ka
Zo mu zauna dake masoyiya
Na amince da ke muyi auren sunnah
Zo mu zauna da kai muyi rayuwa
Na amince da kai muyi auren sunnah

Ni dake zan daura aure
Na zamo ango ke amare
Daki na a gida na zaki tare
Ki rangwada kwaliyar ki sa turare
Farin cikin ki zaya dore
Hawayan ki nine zan share
Da ke zan zauna na more
A tare ba ware
Zana jure
Mu kore ba ware
Allah hore
Kai ne zabi Allah yayi mini
Naji dadi nima kayi mini
Ga hannu na kama ka hayar dani
Gidan aure ka kaini ka, kaini
A mata zai zama babu kamar ni
Domin nasan sai na kece raini
Matsayi mai girma kai zaka kai ni
Zo mu zauna da ke masoyiya
Na amince da ke muyi auren sunnah
Zo mu zauna da kai muyi rayuwa
Na amince da kai muyi auren sunnah

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель