Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - So Haka Yake текст песни

Исполнитель: Umar M. Shareef

альбом: Tsintuwa


Eh-eh-eh-eh
Godiya gurin masani
Sa'a tana nan dani
Iyaye na sun baka ni
A rabu mu sai na bani
Kazo ka dauke ni
Gidan ka, ka kai ni
Idan ka aure ni na zarce wa yanmata
Na waro ki cikin mata ke nayi zaba
Mai kyawun natsuwa halin naki baki kwaba
Ba kya raina abun da na baki na so ki karba
Harsashen ki da yayi tsalle rai na ya harba
Shi yasa duk inda na gan ki gurin zan raba
Auren ki in nayi hakika ni na caba
Yadda ka furta haka nima nawa a zahiri ma yafi
Soyayyar da nake maka nayi natso ciki nayi zurfi
Wane Juliet a matakin so ku hada mu tabbas na fi
Ba ni hada ka da kowa zani rufe ka in sa murfi
Littafi zan tsara in yi yabon ka shafi-shafi
In dinga karanto ma so in zuga ka suka karin karfi
Kin shiga kin samu wuri kin zauna kin zauna yanmata
Zana rike ki hannu biyu alkawari zan miki gata
Ka shiga raina ka samu wuri ka zauna
Zana rike ka hannu biyu alkawari zan maka gata
Da jin haka na gode kalaman ki
Idanu na bude ina kallon ki
Kin san ya na rude na kara son ki
Ina yin shauki dalilin ki
Ni zan hau doki in goya ki
Kin kwashe maki kin iya tuki, ga ni a motar ki
Za ni yabe ki, kin iya mulki, ga ni a fadar ki
Ni zan iya yaki dalilin ki matata
Kin shiga kin samu wuri kin zauna kin zauna yanmata
Zana rike ki hannu biyu alkawari zan miki gata
Ka shiga raina ka samu wuri ka zauna
Zana rike ka hannu biyu alkawari zan maka gata

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель