Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Meera текст песни

Исполнитель: Umar M. Shareef

альбом: Tsintuwa


Meera Meera (ahhh)
Meera Meera (ahh)
Meera Ameerah (ahh)
Kin shiga zuciya da raina meera
Bani zuma ta so in sha don wakar ki zanyi yanzu
Kai na saka a zuciyata meera
Amshi zuma ta sok muyi waka yanzu yanzu
Bani zuma in sha kyauta ta masoya
Za ta saka na kara zaki daga murya
In nayi baituka da kyau ke kika sanya
Za na yabe ki gimbiya ke sanadin farin ciki na
Za na yabe ka saurayi kaine farin ciki na
Kin shiga zuciya da raina meera
Bani zuma ta so in sha don wakar ki zanyi yanzu
Ka shiga zuciya kuryar ta ka kwanta
A gadon ka na karbi kaunar ka wacca kauna ta kafata
Ko guduma da bindiga basu cire ta
Kai sha'anin ka kai miji watarana kai miji na
Kiyi sha'anin ki yar budurwa kece farin cikina
Kai na saka a zuciyata meera
Amshi zuma ta so sha muyi waka yanzu yanzu
Bana ruwan ido meera a so ke na zaba
Daidai da gwargwado za na kula ki babu kwaba
Muje filin cido za na tsaya bazan guje ba
Sai nayi hubba, ko ban iya ba
Jarunta ta zana nuna koda zan rasa raina
Jarunta ta zana nuna saboda so da kauna

Kin shiga zuciya da raina meera
Bani zuma ta so in sha don wakar ki zanyi yanzu
Ado na tafiya waiwaye kai na waiga
Duba ina ta yin zagaye nayi yanga
Wankan da nayi ba jirwaye na saka riga
Idan na samu gu nayi shiru kai nake tunawa
Idan na samu gu nayi shiru ke nake tunana

Na tausaya wa mai yin so da ba'a son shi
Kalama ta ki da zafi kama da rushi
Ko'a baki dadi soyayyah ambata shi
Zo ki fada da kanki dadi zai zo kunnuwa na
Zana fadi kayi murna jindadin idanuwana
Kin shiga zuciya da raina meera
Bani zuma ta so in sha don wakar ki zanyi yanzu
Kai na saka a zuciyata meera
Amshi zuma ta so kasha muyi waka yanzu yanzu

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель