Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Ke Na Bida текст песни

Исполнитель: Umar M. Shareef

альбом: Tsintuwa


Na baki soyayya ta
Da baki na furta ta
Wadan su na neman ta
Gare ni ba damar ta
Kina ta yin kyama ta
Shin menene illa ta
Ki so ni zaki huta
Ki yo daban cikin mata
Komai kike bukata
Akwai kudi da mota
Diba ki dinga yin kyauta
Zan baki dukkanin gata
Ke na bida
Kin ce, "Ban miki ba"
Sai ki fada
Mecece matsala ta a soyayya
Ke na bida
Kin ce, "Ban miki ba"
Sai ki fada
Mecece matsala ta a soyayya

Soyayya ta gaske da gaskiya
Ba karya kudi basa iya siya
Tarbiyya ta hana jayayya
Sun raba hanya, arziki da tsiya
Ni ban ki kaba
Kuma bazan so ka
Muyi mararraba
Da juna sam bamu dace ba
Ba kayi mini ba
Kuma ba zaka yi mani ba
Barni inyi gaba
Ina da wanda nake so da soyayya
Ba kayi mini ba
Kuma ba zaka yi mani ba
Barni inyi gaba
Ina da wanda nake so da soyayya

Dan gayu nake
Ko a cikin su daban nake
Yan mata kar kiyi sake
Da karfi ni zaki rike
Ki yarda mu zauna dake
Matata ni ince dake
In munyi aure dake
Zan baki kula har ace baya ke
Nidai ke na bida
Kin ce, "Ban miki ba"
Sai ki fada
Mecece matsala ta a soyayya
Ke na bida
Kin ce, "Ban miki ba"
Sai ki fada
Mecece matsala ta a soyayya
In dai kayi tunani
So bai duban kamanni
Kyawu koko muni
Ra'ayin haka da akwai ni
Inda zaka kyale ni
Inje inyi rayuwata ni
Da wanda nake kauna ni
Kayi min haka ka taimake ni
Ba kayi mini ba
Kuma ba zaka yi mani ba
Barni inyi gaba
Ina da wanda nake so da soyayya
Ke na bida
Kin ce, "Ban miki ba"
Sai ki fada
Mecece matsala ta a soyayya

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель