Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Hasashe текст песни

Исполнитель: Umar M. Shareef

альбом: Tsintuwa

Nayi hasashe
Hasashe
Hasashe na ya tabbata gamu a tare cikin soyayya
In bake sai na jikita yaki taho zo muyi tarayya
Hasashe na ya tabbata gamu a tare cikin soyayya
In bakai sai na jikita yaki taho zo muyi tarayya

Tafiya komai sannu-sannu ake farawa
Dokin hakuri duk wanda ya hau shi yana dacewa
A tsakani in dai an zauna akan sabawa
In an sasanta dai-dai ne shine morewa
Kaina na baki, na zam naki
Kallan da idanun ki
Ya sakan shauki

Kai zan ba zobe, ka saka shi a hannun ka
Bana so mu rabe, ka saka ni a kirjin ka
Kai na kira gwadabe, ka bani takobin ka
In ka ban zani cafe, ammah sai na duka
Biyayya zan nuna, kullum in gaishe ka
Na barsu mahaifa na, na yarje zan bika
Hasashe na ya tabbata gamu a tare cikin soyayya
In bakai sai na jikita yaki taho zo muyi tarayya
Ta daban ce ke ta daban, a ciki ke na ware
Ku raba mu kunyi kadan, in kunka matsa sai kun zare
Mutuwa ne zanyi idan babu ke sai na haure
Lafiya ta kece indai baki kwarai bani
Na tsaya na nace bani gudu sai an bani
Abari ya huce shike bada rabo ga wani
Hasashe na ya tabbata gamu a tare cikin soyayya
In bakai sai na jikita yaki taho zo muyi tarayya

Hasashe na ya tabbata gamu a tare cikin soyayya
In bake sai na jikita yaki taho zo muyi tarayya
Ni taka tun asali ba mai kwace ma
Ji karka so furari shi nayi rokawa
Zani sako kwalli inzo in nuna ma
Kai ka saka ni kiba jikina ba rama
Hankalina ya kwanta
Damuwa tuni na manta da zuwan ka cikin raina (haaa haa)

Idan gaki ba wata mace da zan kalla
Diya babba yar makaranta baki yin talla
Tafiya ta mai nisa a gidan ki zan bulla
Kin kore min komai zai sa nayo kwalla
Hasashe na
Tunani na
Ta nuna manuni gaki nan ga ni
Hasashe na ya tabbata gamu a tare cikin soyayya
In bakai sai na jikita yaki taho zo muyi tarayya

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель