Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Ban Gudunki текст песни

Исполнитель: Umar M. Shareef

альбом: Best Of M Shareef Vol. 1


Ban gudun ki kowani yanayi
Kin ka samu kan ki a nan nake
Ban gudun ka kowani yanayi
In ka samu kan ka a nan nake
Ban gudun ki kowani yanayi
Kin ka samu kan ki a duniya
Ban gudun ka kowani yanayi
In ka samu kan ka a duniya
Zan kula dake, alkawari nayi wa kaina
Na aminta cewa in mutu keko ki zauna
Zani zauna da yunwa keko kici zanyi murna
Ko ana harbi
Ko ana harbi
Ko ana harbi da bindiga zan shigo inzo inda kike

Abinda zaka, ce inyi shi babu ja na sallama
Kasa ni zana yi, ko rafi kace in tsunduma
Nauyi bazan ji ba, ko tsauni kace in kinkima
Ana ruwan sama
Ana ruwan sama
Ana ruwan sama ungo lema, na aminta ni kuma in jike

Indai akwai kula, soyayyah na kara karuwa
Sai anyi shakuwa, ake bayyana wa juna damuwa
Ra'ayi hali daya, shike haifar da jituwa
Na dasa ki a zuciya, babu wata macen da zata zo har ta hake

Sa'a Rabbi shike bayarwa
Soyayyar mu shi yayi hadawa
Hakuri ga wanda ke nemawa
Sannu watarana zai samawa
Addu'a Allah nake ta rokawa
Auren mu za'ayi daurawa
Komai nake bida, babu mai min
Rabbi kai kadai ni na rike
Ban gudun ki kowani yanayi
Kin ka samu kan ki a duniya
Ban gudun ka kowani yanayi
In ka samu kan ka a nan nake

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Bako

2017 · альбом

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель