Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Yaki A Soyyaya текст песни

Исполнитель: Umar M. Shareef

альбом: Best Of M Shareef Vol. 1


Yaki a soyayyah na shirya taho mu buga yan mata
'Yan mata, ah-ah yan mata
Yaki a soyayyah na shirya taho mu buga dan gata
Dan gayu, ah-ah dan gata

In kinka dau kibiya, ni kuma zana dau mashi
Ba zana motsa ba, indai zaki harbo shi
Zan sanya kirji na, ba tsoro in tarbe shi
Cikin zuciyata, ai nan ne masaukin shi
Kinyo nasara a cikin yakin ki dauki shi
Kin zamto sarauniya duk mata kece da kinga gaba manufata
Manufata ah-ah
Gani na isko ka gaba da gudu, in na isko ka sai nishi
Indai da soyayyah, tabbas akwai kishi
Kai dai zana ba rance tunda kana biyan bashi
Ka harbe ni, zana tsaya da harsashi
Na soyayyah, baya kisa koya tashi
Tun ranar da ka same ni dashi jina nake kamar wata autar mata
Autar mata
Sun koma da sun ganki, kin masu kwarjini
Sunyi bugu sun barki, kin sasu hawan jini
Soyayyah ta taki, zo ki kula dani
Indai na aure ki, baki guna-guni
Naji giyar soyayyah, kin shayar dani
Nima dole in baki nawa don kiyi masu rata
Kiyi masu rata

Haduwa ta dakai tayi riba
Lokaci guda munka saba
Ka zamo madubi na duba
Abinda kaso inyi, zanyi shi ba aibu ba
Aure na sanya a rai, dakai ka zamto uba
Mu hado zuri'a dakai shine manufa ta
Manufata
Cikin su mazaze, ai kaine auta na maza
Cikin mataye, ai kece autar mata
Ra'ayi kuma riga, je ki dau dankali ni gwaza
A raina na sanyo ki, na baki kula yar gata
'Yar gata
'Yar gata, ah-ah yar gata
Dan gata ah-ah dan gata
Yaki a soyayyah na shirya taho mu buga yan mata
'Yan mata, ah-ah yan mata
Yaki a soyayyah na shirya taho mu buga dan gata
Dan gayu, ah-ah dan gata

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Bako

2017 · альбом

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель